logo

HAUSA

Yabon gwani ya zama dole

2021-06-29 18:25:27 CRI

Da safiyar yau Talata ne aka gudanar da bikin karramawa tare da bayar da lambar yabo mafi daraja ga ’ya’yan Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da suka bayar da gagrumar gudummawa ga ci gaban jam’iyyar da ma kasar. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ne ya bayar da lambar yabon mafi daraja a tarihi ta “Ranar 1 ga Watan Yuli”, wadda ta kasance irinta ta farko da jam’iyyar ta taba bayarwa.

Cikar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin shekaru 100 da kafuwa ya nuna tarihin gwagwarmayarta tare da irin jajircewarta cikin wadannan shekaru. Kamar yadda burin jam’iyyar ya kasance farantawa da kyautata rayuwar jama’ar kasar, haka su ma burin ’ya’yan Jam’iyyar ke kasancewa hidimtawa ci gabanta. Kuma wannan shi ne tubalin nasarorin da Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin ta samu. Ba za a taba raba nasarori da ci gaban da kasar ta samu da hidima da sadaukarwa jam’iyyar da ’ya’yanta ba. Kishi da sadaukarwarsu ya zama abun koyi ga al’ummar duk wata kasa dake son ci gaba. Ko ina aka shiga a kasar Sin, za a samu akwai fahimta da jituwa tsakanin jam’iyyar da ’ya’yanta. Sannan amincin da suke nuna mata ba tare da shakku ba, ya sa ita ma take jajircewa wajen ganin ta rike alkawarinta na faranta musu. Lallai Jam’iyyar kwaminis ta yi hangen nesa wajen zabarwa kasar irin tsarin da ya dace da ita, tare da jajircewa wajen sanya kishi a zukatan al’umma. Muddun tsarin shugabanci ya kasance mai sanya walwalar al’umma da kare muradu da ’yancinsu a gaban komai, to dole ne su ma al’umma su ba ta cikakken goyon baya. Wato ana iya kiran dangantakar dake tsakanin jam’iyyar da ’ya’yanta a matsayin irinta “saka alkhairi da alkhairi”.

Duk da cewa ba dare daya kasar Sin ta kai matsayin da take ba, al’ummarta sun yi hakuri tare da ba ta goyon baya. Lallai ’ya’yan jam’iyyar sun kasance abun koyi ga al’ummomin kasa da kasa, domin sun nuna cewa, neman ci gaba da samun zaman lafiya ba hakkin ne da ya rataya a kan gwamnati kadai ba, abu ne dake bukatar dukkan wani mutum ya ba da tasa gudunmawa ta hanyar da zai iya.

Lambar karramawar irinta ta farko, za ta nunawa mambobin jam’iyyar cewa, uwar jam’iyyar na sane da irin gudunmawar da suke bayarwa, lamarin da zai kara zaburar da su, haka kuma ya zaburar da zuri’a masu tasowa wajen dorawa kan ayyukan da magabantasu suka yi.

Da yake jawabi yayin bikin karramawar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ce a sabon zamanin da ake ciki, ana bukatar jarumai, haka kuma, ya kamata jam’iyyar kwaminis ta zama jigon ci gaban zamani, kana kashin bayan daukacin al’umma.

Babu shakku cewa mambobin jam’iyyar za su ci gaba da kasancewa jarumai, domin sun riga sun nuna hakan. Kana ai tuni jam’iyyar ta zama jigon ci gaban zamani, bisa la’akari da yadda a karkashinta, kasar Sin ta samu ci gaba har ma take kokarin tallafawa sauran kasashe masu tasowa wajen samun ci gaba. Hakika kasar Sin karkashin jagorancin Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ta zama jagora kuma abun koyi ga daukacin kasashen duniya da al’ummominsu. (Faeza Mustapha)