logo

HAUSA

Wei Wei, wani matashi dan kasar Sin wanda ya halarci aikin raya Afirka tsawon shekaru 13

2021-06-28 14:08:54 cri

Wei Wei manajan sashen aikace aikace ne, na wani kamfanin kasar Sin dake Zimbabwe. A matsayinsa na mai shiga cikin ayyukan "fita waje" na kamfanonin kasar Sin, kuma maginin aikin "Ziri daya da hanya daya", ya yi ta yi aiki a Afirka har tsawon shekaru 13.

A filin jirgin saman kasa da kasa na Robert Mugabe da ke Harare, babban birnin kasar Zimbabwe, Wei Wei na aiki a sashen Kamfanin hadin kan tattalin arziki da fasahohi na kasa da kasa na Jiangsu dake kasashen waje, yana jagorantar rukuninsa don gyara, fadadawa, da gina filin jirgin saman na Robert Mugabe, don ya zama cibiyar sufurin jiragen sama ta zamani a Zimbabwe, wanda zai iya daukar karin hanyoyin jiragen sama. Wei Wei ya bayyana cewa, 

“A matsayinsa na babban aikin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin kasar Sin da ta Zimbabwe, sake ginawa da fadada filin jirgin sama na Harare, zai inganta yanayin kasuwancin Zimbabwe gaba daya, da kuma ingancin filayen jiragen saman farar hula, gami da kyautata yanayin aiki a filin jirgin. Duk da cewa, filin jirgin saman Harare aiki ne na sake gini da fadadawa, tsohon filin jirgin saman har yanzu yana aiki, don haka, lokacin da muke gina sabon bangaren filin jirgin, bai kamata aikin ya shafi ayyukan da ake yi a bangaren tsohon filin jirgin ba. Wato akwai bubatar ci gaba da gini ba tare da tsayar da aikin daya sashen ba. Hakan ya sa muke fuskantar babban hadari da wahalhalu masu tarin yawa, wajen gudanar da wannan aikin.”

Wajibi ne a yi kokarin tabbatar da ci gaban aikin ginin ba tare da kawo tasiri ga aikin filin jirgin na yau da kullun ba. Wei Wei ya jagoranci kungiyarsa don fuskantar wannan aiki mai wuyar gudanarwa. Sun dauki hanyar gudanar da aikin ginawa ba tare da tsayar da aiki a filin jirgin saman ba da dare, kuma sun kammala aikin gyaran titin jirgin sama bisa ma’auni da inganci mai kyau cikin lokaci. Wei Wei ya ce,

 “Muna aiki na kimanin sa’o’i biyar ko shida a kowane dare. Muna amfani da na’urori guda 80, don gudanar da aiki bisa matakai daban-daban. Hakan yana bubatar cewa, dole ne mu kasance masu karfi wajen tsara aiki, kuma mu yi kyakkyawan shirin amsawa a fannonin inganci da tsaro, ta yadda hakan zai tabbatar da kammalar ayyukanmu yadda ya kamata.”

Wei Wei, wani matashi dan kasar Sin wanda ya halarci aikin raya Afirka tsawon shekaru 13_fororder___172.100.100.3_temp_16_1_16_1_1_d50dd32c-b79a-44fe-b17a-faae90fa1c58.JPG

Wei Wei ya yi ta yi aiki a kasar Zimbabwe fiye da shekaru 9, kuma ya shiga cikin ayyukan gina filayen jirgin saman Zimbabwe guda biyu. Musamman ma aikin sake gina filin jirgin sama na Victoria Falls, sanannen birni mai albarkatun yawon bude ido a kasar ta Zimbabwe, wanda hakan ya ba shi damar samun lambar yabo ta kungiyar injiniya ta Zimbabwe a shekarar 2016. Ba za a iya cimma wannan nasara ba, sai dai Wei Wei da abokan aikinsa su kan yi kokarin kirkiro sabbin fasahohi da kuma tinkarar wahalhalun dake kasancewa a gabansu ba tare da kasala ba. Wei Wei ya ce,

“A wancan lokacin, akwai bukatar da mu gina wani titin jirgin sama mai tsawon kilomita 4 da fadi na mita 60 a birnin Victoria. Aikin na bukatar kananan duwatsu da yawa. Amma babu wuraren fasa duwatsu kusa da birnin. A bisa taimako daga Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama, da kuma Ma'aikatar sufurin kasar, mun tafi Hwange dake da nisan kilomita 100 daga magangarar ruwa, wanda kuma cikin duwatsu ne dake daji, don binciko ma'adinai. Mun yi wasu lokuta muna samun ma'adanan da suka fi dacewa, kuma daga karshe dai mun gina filin haka duwatsu, don tabbatar da samar da kananan duwatsu masu inganci ga aikin gina titin jirgin sama, sannan mun tabbatar da gudanar da aikin yadda ya kamata.”

Tawanda Gusha, mukaddashin shugaban kamfanin jiragen sama na Zimbabwe ya nuna yabo ga Wei Wei cewa,

 “Ya zuwa yanzu, muna gamsu da ci gaban da aka samu daga aikin da ake yi a filin jirgin saman kasa da kasa na Harare. Wei Wei da tawagarsa, suna gudanar da aikin bisa babban ma’uni da inganci mai kyau. Muna kuma gudanar da hadin kai tare da Wei Wei yadda ya kamata, abin da na fi son nuna yabo shi ne, yadda yake fuskantar matsaloli, yana cika alkawuran da ya dauka, kuma ya yi aiki tukuru domin kokarin sauke nauyin dake bisa wuyansa.”

Bayan ya yi shekaru 10 ko fiye yana aiki a ketare, Afirka ta zama gari na biyu ga Wei Wei. A wannan nahiya mai cike da fata tare da kalubale, Wei Wei ya sadaukar da kuruciyarsa, da bajinta don gina Afirka, da tabbatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya". (Bilkisu)