logo

HAUSA

Juma’a Mai Kyau Tun Daga Laraba Ake Gane Ta

2021-06-28 16:41:36 CRI

Juma’a Mai Kyau Tun Daga Laraba Ake Gane Ta_fororder_0628-01

Yayin da a ranar 1 ga watan Yuli mai kamawa za a shiga ranar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin CPC, yanzu dai hankalin duniya ya karkata game da wannan mashahurin biki mai dunbun tarihi. Koda yake, shugabannin kasa da kasa, jami’an diflomasiyya, da masu fashin baki kan al’amurran siyasar duniya suna ta bayyana ra’ayoyinsu da tsokaci kan batun cikar jam’iyyar ta JKS shekaru 100 da kafuwa da kuma muhimman nasarori da ci gaban da kasar ta Sin ta cimma cikin wadannan shekaru. Alal misali, a karshen wannan mako, babban darektan cibiyar kafafen yada labaran Afirka da Sin dake Najeriya, Mista Ikenna Emewu, ya wallafa wani sharhi mai taken “Kasar Sin Karkashin Jagorancin Jam’iyyar Kwaminis a Shekaru 100” a jaridar The Nation ta kasar, inda ya bayyana ra’ayinsa cewa, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta jagoranci kasar wajen lalibo hanyar juyin-juya-hali da samar da ci gaba, da jagorantar al’ummar kasar su tashi tsaye don samun wadata, kana ta bayar da babbar gudummawa wajen shimfida zaman lafiya da samar da ci gaba a duk duniya baki daya. Sharhin ya ce kasar Sin ta samu dimbin nasarori karkashin jagorancin jam’iyyar kwaminis ta kasar, har ma ta kai matsayin kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya. A shekara ta 2020, yawan GDPn kasar ya zarce kudin Sin Yuan triliyan 100, ta fitar da mutane kusan miliyan 800 daga kangin talauci, ta bayar da gudummawar kaso 92 bisa dari ga ayyukan rage talauci a duniya. Har ma kasar Sin ta dauki matakan yaki da cutar COVID-19 yadda ya kamata wajen dakile yaduwar cutar, kana ta yi nasarar samar da alluran riga-kafin cutar da taimakawa ayyukan yaki da cutar a duk duniya. Shi ma tsohon shugaban kasar Namibiya yana da ra’ayin cewa, manufar mayar da ci gaban rayuwar al’umma a gaban komai na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS, ba kawai ya amfanawa al’ummun Sinawa kadai ba ne, har ma da al’ummun duniya baki daya, Sam Nujoma, ya taya babban sakataren kwamitin tsakiyar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, da kwamitin tsakiyar jam’iyyar ta JKS, da dukkan al’ummun Sinawa murnar cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar ta JKS, inda ya yabawa muhimmin tarihin da ta kafa da manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma. Sanannen dan siyasar kasar ta Namibia ya ce, kasar Sin ta kasance a matsayin kasar da tattalin arzikinta yake saurin bunkasa a duniya, kuma jam’iyyar CPC ce ta tsara dabarun da suka taimakawa kasar wajen samun muhimman nasarori a yaki da annobar COVID-19, da yaki da talauci, da kuma yadda tattalin arzikin kasar ke bunkasa, gami da kyautatuwar yanayin zaman rayuwar al’ummar kasar. Ko shakka babu, yabon gwani ya zama dole, domin kuwa a halin yanzu jam’iyyar JKS tana shan yabo daga shugabannin kasashen duniya, da hukumomin kasa da kasa, gami da masu nazari da sharhi kan al’amurran siyasar duniya bisa rawar da jam’iyyar ta taka da yadda ta kudiri aniyar tabbatar da bunkasuwar duniya da samar da makoma mai kyau ga dukkan bil adama, da irin rawar da take takawa wajen gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil adama da kuma gabatar da sabbin manufofin kyautata mu’amalar kasa da kasa, musamman manufar nan ta hadin gwiwar bangarori daban daban domin a gudu tare a tsira tare. (Ahmad Fagam)