logo

HAUSA

Ya kamata Japan ta soke aniyarta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku

2021-06-26 21:16:35 CRI

Ya kamata Japan ta soke aniyarta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku_fororder_A

A wajen taro na 31 tsakanin kasashen da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar dokar ruwan teku ta Majalisar Dinkin Duniya wanda aka yi jiya Jumma’a, wakilin kasar Japan ya yi jawabi cewa, wai zubar da ruwan dagwalon nukiliya da aka riga aka tace shi zuwa teku ba shi da illa, kuma Japan ba ta rufe komai ba, har ma ta riga ta samu amincewa daga hukumar makamashin nukiliya ta duniya wato IAEA.

To sai dai idan da gaske ruwan dagwalon nukiliyar ba shi da illa ko kadan, bayan da aka tace shi, ya dace kasar Japan ta amsa wannan tambayar, wato me ya sa ta kuduri aniyar zubar da ruwan cikin teku maimakon amfani da shi a kasar?

Sanin kowa ne, wani hadari mafi tsanani ya taba faruwa a tashar makamashin nukiliya ta Fukushima dake kasar Japan, abun da ya sa ruwan dagwalon nukiliya da aka fitar daga tashar yana dauke da abubuwa masu guba da yawa, wanda ya bambanta kwarai da ruwan da aka fitar daga cikin sauran tashoshin makamashin nukiliya masu aiki yadda ya kamata, kuma ba’a taba samun wata kasar da ta yi haka ba a duniya, ita Japan ma ba ta da wannan fasaha.

Ya kamata Japan ta soke aniyarta na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku_fororder_B

Har wa yau, hukumar IAEA ba ta taba amincewa da kudurin Japan na zubar da ruwan dagwalon nukiliya cikin teku ba. A halin yanzu, hukumar tana kokarin kafa wani rukuni na musamman da zai kunshi kwararru daga kasashen Sin da Koriya ta Kudu don gudanar da bincike.

Yadda za’a yi domin daidaita ruwan dagwalon nukiliya daga tashar Fukushima, ba harka ce ta Japan kadai ba. Kuma kididdigar da cibiyar nazarin kimiyyar ruwan teku ta kasar Jamus ta fitar ta nuna cewa, tun daga ranar da aka zubar da ruwan, a cikin shekaru 10 masu zuwa, zai yadu zuwa yankin ruwan teku na duk fadin duniya, al’amarin da ko shakka babu zai haifar da mummunar illar da ba za’a iya kiyastawa ba ga muhallin yankin teku da tsaron abinci gami da lafiyar dan Adam.

Ya zama dole kasar Japan ta dakatar da kitsa karairayi ta girmama ka’idojin duniya, ta soke kudirinta na zubar da ruwan dagwalon nukiliyar a cikin teku. (Murtala Zhang)