logo

HAUSA

Yan siyasan kasashen yamma na neman bata yanayin zaman lumana a HK bisa hujjar ’yancin labarai

2021-06-25 16:11:26 CRI

Yan siyasan kasashen yamma na neman bata yanayin zaman lumana a HK bisa hujjar ’yancin labarai_fororder_210625-sharhi-Maryam-hoto

Bayan da aka sanar da dakatar da harkokin jaridar “Apple Daily”ta yankin Hong Kong na kasar Sin, aka kuma rufe shafinta na intanet, wasu ‘yan siyasar kasashen yammacin duniya da suka hada da kasar Amurka, da kasar Burtaniya da sauransu, suka fara zargin kasar Sin da cewa, ta hana ‘yancin watsa labarai. To sai dai kuma wannan zargi ne maras tushe, domin kuwa an dakatar da harkokin jaridar “Apple Daily” ne bisa laifin keta dokar tsaron yankin Hong Kong.

Wadannan ‘yan siyasa na kasashen yammacin duniya suna zargin Sin, da hujjar kare ‘yancin watsa labarai, domin tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, lamarin da ya keta dokar kasa da kasa, da ka’idojin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa. Shi ya sa, mutanen yankin Hong Kong, da ma dukkanin al’ummomin kasar Sin, ke nuna adawarsu da kakkausan harshe, kan yadda wadannan ‘yan siyasa suke neman tsoma baki cikin harkokin gidan kasar Sin, da kuma bata yanayin zaman lumana a yankin Hong Kong na kasar.

Bisa labarin da ‘yan sandan yankin Hong Kong suka gabatar a baya bayan nan, a ranar 18 ga wata, ofishin kare tsaron yankin Hong Kong na kasar Sin, ya gabatar da korafi kan jaridar “Apple Daily” ta Hong Kong, bisa laifin keta dokar tsaron yankin Hong Kong, ta hanyar tuntubar mutanen da suke ketare, da nufin gurgunta yanayin tsaron kasa.

Daga karshe dai an dakatar da harkokin jaridar, da kuma rufe shafinta na intanet bisa doka yadda ya kamata, kuma bai dace wadannan ‘yan siyasa na kasashen yammacin duniya su rika tsoma baki cikin wannan harka ba. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)