logo

HAUSA

Sin ta goyi bayan Argentina kan kare ikonta na mallakar tsibiran Malvinas

2021-06-25 20:52:21 CRI

Sin ta goyi bayan Argentina kan kare ikonta na mallakar tsibiran Malvinas_fororder_AAA

Jiya Alhamis, a wajen taron kwamitin musamman na kawar da mulkin mallaka na Majalisar Dinkin Duniya, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin dake majalisar, Geng Shuang ya yi jawabi kan batun tsibiran Malvinas, inda ya tsaya kan marawa kasar Argentina baya, game da bukatar ta na kiyaye ikon mallakar tsibiran, gami da fatan kasar Birtaniya za ta amsa kiran Argentina, ta gaggauta farfado da shawarwari, a wani kokari na lalubo bakin zaren daidaita matsalar bisa kudurin MDD.

A yayin da Birtaniya take fadada mulkin mallaka a yankin kudancin Amurka, ta kwace tsibiran Malvinas bisa karfin soja a shekara ta 1833. A shekara ta 1965, MDD ta zartas da kudiri, inda ta yi kira a kawar da mulkin mallakar da aka yi a wajen, da bukatar Birtaniya da Argentina na daidaita rikicin ta hanyar yin shawarwari.

Batun tsibiran Malvinas, batu ne da ya shafi tarihin mulkin mallaka. Kuma bayan yakin da aka yi tsakanin Birtaniya da Argentina kan tsibiran, Argentina ba ta taba daina bayyana bukatar ta na neman samun mulkin kai a wurin ba. Har ma kwamitin kawar da mulkin mallaka na MDD ya bukaci gwamnatin Birtaniya ta gudanar da shawarwari tare da gwamnatin Argentina, amma Birtaniyar ta ki amincewa.

Waiwaye adon tafiya. Idan ba mu iya fuskantar tarihi yadda ya kamata ba, ba za mu iya fuskantar yanzu da nan gaba ba. A halin yanzu, siyasar nuna danniya da babakere da ta samu asali daga mulkin mallaka na ci gaba, da ciwa al’umma tuwo a kwarya a duk fadin duniya, musamman kasashe masu tasowa, ciki har da tsoma bakin da Birtaniya ta yi cikin harkokin yankin Hong Kong, da mulkin mallaka a fannin yanayi da manyan kasashen yammacin duniya suka yiwa kasashe masu tasowa.

Ya dace kasa da kasa su zama tsintsiya madaurinki daya, don ci gaba da taimakawa ayyukan kawar da mulkin mallaka, a wasu yankunan da ba na cin gashin kansu ba guda 17, ciki har da tsibiran Malvinas. (Murtala Zhang)