Umar Danladi Dahiru: Muhalli shi ne lamba daya a harkar rayuwa
2021-06-25 22:37:04 CRI
Matsalar kwararowar hamada da fari, tana barazana ga rayuwar alumma, da ma ci gabansu, a kaso biyu daga cikin uku na kasashe da shiyyoyin duniya, ciki har da kasar Sin, da ma wasu kasashen Afirka.
Cikin shirinmu na yau, mun samu damar tattaunawa tare da malam Umar Danladi Dahiru, wanda shi ne darektan cibiya mai rajin kare kwararowar hamada a kasashen Afirka da ke Nijeriya, don jin ta bakinsa, game da kalubalen da ake fuskanta, da ma hadin gwiwar da Sin da Nijeriya suka aiwatar, ta fannin kare kwararowar hamada.