An kaddamar da shirin raya unguwannin kiyaye muhalli a kasar Mexico
2021-06-24 10:22:41 CRI
An kaddamar da shirin raya unguwannin kiyaye muhalli a kasar Mexico. Ana sa ran cewa, ta wannan shiri mai suna Living The Noom, gine-gine uku za su samar wa kansu kaso 85 cikin dari na makamashin da suke bukata, ta hanyar tattara ruwan sama, da dasa bishiyoyi, da ma amfani da na’urorin samar da wutar lantarki masu aiki da harsken rana.