logo

HAUSA

Shirin kasar Sin na raya kauyukan kasar

2021-06-23 08:27:42 CRI

A kwanakin baya ne, mahukuntan kasar Sin suka sanar da aniyarsu ta kara kaimi wajen ganin an hanzarta raya muhimman gundumomin kasar dake samun tallafi, a kokarin da mahukuntan kasar ke yi na raya kauyuka.

Shirin kasar Sin na raya kauyukan kasar_fororder_20210623世界21023-hoto1

Wannan ne ma ya sa, Hu Chunhua, mataimakin firaministan kasar Sin, kana mamba a hukumar siyasa ta kwamitin koli na JKS, ya yi kira da a kara zage damtse, don ganin an karfafa nasarorin da aka cimma wajen kawar da talauci, tare da tabbatar da cewa, ba a bar dukkan gundumomin kasar a baya ba, a kokarin da ake yi na farfado da kauyukan kasar.

Alkaluma na nuna cewa, baki dayan yanayin ci gaban tattali arziki da jin dadin jama’ar gundumomin kasar Sin, yana mataki na kasa, tun bayan da kasar ta yi nasarar kakkabe matsalar kangin talauci. A don haka, akwai bukatar dora muhimmanci kan wannan aiki, wajen kula, da fadada nasarorin da aka cimma a fannin rage radadin talauci.

Mahukunta sun bayyana cewa, ya kamata a kara yawan kudin shigar mutanen da suka fita daga kangin talauci, da kara yawan tallafin da ake baiwa masana’antu dake yankunan da suka ci gaba, da kara ci gaban tattalin arzikin yankunan.

Shirin kasar Sin na raya kauyukan kasar_fororder_20210623世界21023-hoto2

Bugu da kari, akwai bukatar a hanzarta daukar matakan raya jin dadin jama’a da al’adun gundumomin, gami da raya ilimi da hidimomi na kiwon lafiya. Sauran matakan raya kauyukan, sun hada da kara aikin zakulo masu basira dake zaune a kauyuka, da inganta tsarin kula da tsarin gidaje wadanda haka, zai kai taimaka wajen hanzarta zamanantar da aikin gona, da kayayyakin more rayuwa da kirkire-kirkire a fannin aikin gona.

Masu fashin baki na ganin cewa, matakan kasar Sin ta raya fifikon yankuna, da samar da ababan more rayuwa da sabbin fasahohin zamani, za su taka muhimmiyar rawa ga shirin kasar na raya baki dayan yankunan karkarar kasar kamar yadda aka tsara. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)