Jami’ai da masanan Kenya: JKS ta samar da babbar gudummawa ga kokarin samun ci gaban dan Adam
2021-06-23 12:25:12 CRI
A kwanakin baya, an gudanar da taron tattaunawa mai taken “cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta Sin: fasahohin da JKS ta samu yayin gudanar da harkokin kasar” a birnin Nairobi dake kasar Kenya, inda jami’ai da masana da dama na kasar Kenya suka bayyana cewa, JKS ta samar da babbar gudummawa wajen sa kaimi ga samun ci gaban dan Adam.
A jawabinsa, direktan ofishin kula da harkokin waje na jam’iyyar Jubilee ta kasar Kenya John Mutinda Mutiso, ya taya jam’iyyar kwaminis ta Sin murnar cika shekaru 100 da kafuwarta, kana ya yabawa JKS kan yadda ta jagoranci jama’ar kasar Sin wajen kirkiro da abubuwan ban al’ajabi a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’umma. Mutiso ya bayyana cewa, a matsayinta na jam’iyyar dake mulki a kasar Kenya, jam’iyyar Jubilee, ta amince tare da imani da matakan da JKS ke dauka wato dora muhimmanci kan jama’a, da daukar tsauraran matakai wajen gudanar da harkokin jam’iyyar, a ganinta, wannan shi ne muhimmin dalilin da ya sa JKS ta iya jagorancin kasar Sin wajen samun babban ci gaba. Mutiso ya ce,
“A bisa jagorancin babban sakataren JKS Xi Jinping, Sin ta samu manyan nasarori a fannin bunkasa zamantakewar al’ummar kasar a sabuwar shekara. Mun ga cewa, an yi nasarar fitar da mutane miliyan 700 daga kangin talauci, an cimma wannan nasara ne, saboda tunanin JKS na samun bunkasuwa bisa yanayin da ake ciki, da kuma bin hanyar da ta dace da yanayin bunkasuwar kasar. A halin yanzu, Sin ce kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, kana ta kasance muhimmin karfi a duniya a karni na 21. JKS da shugabannin jam’iyyar sun aza tubalin bunkasa daukacin bil Adam.”
Shugaban cibiyar nazarin manufofin Afirka Peter Kagwanja yana ganin cewa, bisa ra’ayi na kashin kai, da ba da kariya da sauransu, JKS ta cimma nasarar jagorancin Sin wajen samun zaman lafiya da bunkasuwar tattalin arziki da kawar da talauci, don haka ta kasance muhimmin karfi wajen sa kaimi ga tabbatar da odar duniya bayan abkuwar yaduwar cutar COVID-19 a duniya, kuma tana kokarin martaba ra’ayin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da daukar matakai don sa kaimi ga yin hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa a duniya. Ya ce,
“JKS ta kasance jam’iyya mafi girma a duniya. Ta kuma jagoranci Sin wajen tinkari kalubalen da suka kunno kai a karni na 21, wadda ta yi suna a ciki da waje. Yayin da ake tinkarar ra’ayin kashin kai, da tsarin raya duniya na bai daya, shugabannin jam’iyyar sun tsara sabbin manufofin harkokin waje, wadanda za su taimaka ga yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da sauran kasashen duniya.”
A nasa jawabin, jakadan Sin dake kasar Kenya Zhou Pingjian ya bayyana cewa, tushen raya tsarin gurguzu mai hallayar musamman ta kasar Sin, yana da nasaba da jagorancin JKS, da fahimtar manufofin bunkasa Sin da tafiyar da harkokin kasar, muhimmin aiki shi ne a nazarci tarihin kasar Sin da na JKS yadda ya kamata. A cikin shekaru 100 da suka gabata, JKS ta yi kokarin yin kwaskwarima, da maida hankali ga jama’a, kuma ba ta sauya yadda ta ke martaba tunaninta ba. JKS ta yi amfani da tunaninta da ka’idojinta wajen hada kan jama’ar kasar Sin waje guda, don yin kokari tare wajen samun moriya tare. Wannan ya sa, Sinawa suke iya warware matsaloli da daidaita duk wani irin mawuyacin hali da suka tsinci kansu tare. Ya ce,
“JKS jam’iyya ce da ta taimakawa jama’a wajen samun zaman jin dadi, da kuma taimakawa daukacin dan Adam wajen samun ci gaba. Muradun JKS su ne neman jin dadin zaman jama’a, da samun farfadowar al’ummar kasar, da yin hadin gwiwa a duniya. JKS tana son kara yin mu’amala tare da sauran jam’iyyun kasa da kasa, da more fasahohi, da yin shawarwari, tana kuma son yin kokari tare da jama’ar kasa da kasa, a kokarin gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil’adama da ma duniya baki daya.” (Zainab)