logo

HAUSA

Na Gaba Ya Yi Gaba

2021-06-23 17:32:14 CRI

Na Gaba Ya Yi Gaba_fororder_A

A bana ne, JKS take cika shekaru 100 da kafuwa. Jami’iyyar da ta fara da mambobi kalilan, yanzu ta kasance jam’iyya mafi yawan mambobi da girma a duniya. Haka kuma JKS ta zama jam’iyyar da ta yi nasarar jagorantar al’ummar Sinawa wajen tsame baki dayan jama’arta daga kangin talauci, cikin wani wa’adi da ya baiwa duniya mamaki matuka.

Sai dai a yayin da wasu kasashen duniya ke taya kasar Sin murnar cikar wannan babbar jam’iyya shekaru 100 da kafuwa, da ma tarin nasaroin da kasar ta cimma karkashin jagorancinta, wasu kasashen yamma da ’yan kanzaginsu, na nuna adawa da manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma, har ma suke neman bata sunanta da yada karaikayi kan wasu manufofi da take dauka a wasu yankunanta, don neman cimma burinsu na siyasa. Sai dai bakin Alkalami ya riga ya bushe.

Bugu da kari, ci gaban da kasar Sin ta samu karkashin jagorancin JKS, ya sa a duk wani taron kasa da kasa da aka shirya, maimakon tattauna jigon taron don amfanin duniya baki daya, sai mahalartansa, karkashin wasu kasashen yamma, su karkata ga neman bata sunan kasar Sin, a wasu lokutan ma da hana kamfofinta ci gaba. Misali taron kungiyar G7 da na sauyin yanayi da taron lafiya na duniya da sauransu, irin wadannan makiyan kasar Sin, suka rika bullo da abubuwan da ba su ne manufar shirya wadannan taruka ba, duk don neman bata sunan kasar Sin.

Na Gaba Ya Yi Gaba_fororder_B

Ai dama, gaskiya ba ta buya, a yayin taron hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 47, wasu kasashe sama da 60, karkashin wakilin kasar Belarus, sun nuna goyon bayansu ga kasar Sin, kan matakan da take dauka na kare ’yanci da tsaro da muradunta na neman ci gaba cikin lumana, inda ya jaddada cewa, ya kamata a rika girmama ’yanci da mulkin kai na kowace kasa bisa ka’idar kasa da kasa, bai kamata a tsoma baki a harkokin cikin gidan wata kasa ba. Wannan ya nuna cewa, ba a taru aka zama daya ba.

Har kullum kasar Sin tana kira a martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa da ya dace da yanayin da suke ciki, da daina tsoma baki a harkokin cikin gidan kasashe, da martaba ka’idar alakar kasa da kasa, ta yadda za a gina al’ummma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil-Adama. A don haka, burin masu neman hana ci gaban kasar Sin ba zai yi nasara ba. (Ibrahim Yaya)