logo

HAUSA

Dole ne kasar Amurka ta ba da amsa kan batutuwa uku

2021-06-23 20:16:30 cri

Duk da karin tabbatattun shaidu da aka samu, wasu 'yan siyasar kasar Amurka da ke adawa da kasar Sin, har yanzu suna yin karya kan asalin cutar numfashi ta COVID-19.

A kwanan baya, mai ba shugaban Amurka shawara kan harkokin tsaro Jake Sullivan, ya bayyana a wata hira cewa, idan har kasar Sin ba ta kara binciken asalin cutar ba, to za ta fuskanci "Wariya daga kasashen duniya." A nata bangaren kuma, sakatariyar yada labarai ta Fadar White House Jen Psaki, ta yi barazanar cewa, wai kasar Amurka da kawayenta, za su hada kai tare, don matsa wa kasar Sin lamba yadda ya wajaba.

Game da batun gano asalin cutar, 'yan siyasar Amurka ba su cancanci yin mugun fata, da tilasawa kasar Sin ba, kuma Amurka ba ta da ikon matsa lamba ga kasar Sin a madadin al'ummomin duniya. A cikin 'yan kwanakin nan, kasar Sin ta yi kira da babbar murya, da a gudanar da cikakken bincike game da asalin cutar a Amurka, da dalilan da suka sa aka yi sakaci da aikin dakile cutar, da bincike kan wadanda ke da alhakin aikin, da kuma matsalolin da suka shafi dakunan gwaje-gwajen na Amurka sama da 200 dake kasashen waje, ciki har da na Fort Detrick. Wannan ya bayyana ra’ayin duniya game da haka.

Sau biyu kasar Sin ta gayyaci Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) don ta zo kasar Sin, ta yi binciken asalin cutar, amma har yanzu Amurka ba ta bude kofa ga hukumar ba. Maimakon haka ta yi barazanar cewa, wai kasashen duniya za su "ware kasar Sin"!

Yanzu dai, wadda ta boye hakikanin hali ita ce Amurka, wadda ke haifar da matsala ga masana kimiyya, kuma ita ce ke dakile aikin gano asalin cutar, kana tana lalata hadin gwiwar duniya kan yaki da annobar, da kuma dora laifi kan saura. Dole ne kasar Amurka ta amsa kiraye-kirayen uku da kasar Sin ta yi, in ba haka ba za ta fuskanci "Wariya da kasashen duniya." (Mai fassara: Bilkisu Xin)