logo

HAUSA

MDD; Annobar COVID-19 ta tsananta matsalar jin kai a yankin kahon Afirka

2021-06-22 10:05:22 CRI

MDD; Annobar COVID-19 ta tsananta matsalar jin kai a yankin kahon Afirka_fororder_210622-famine in Horn of Afirka

Shirin samar da abinci na duniya (WFP) da kungiyar kula da kaunar jama’a ta duniya (IOM) sun bayyana cikin wani rahoton hadin gwiwa da suka fitar a Nairobin Kenya jiya Litinin cewa, yankin kahon Afirka na fama da matsalar jin kai, da ake dangantawa da tasirin annobar COVID-19 kan ’yan kwadago, da harkokin cinikaya, da aikin raba tallafin abinci.

A cewar rahoton, “Rayuwa sakamakon annobar COVID-19: Yunwa, da kaunar jama’a da raba jama’a da muhallansu a yankin gabashi da kahon Afirka”, annobar ta shafi galibin fararen hula dake sassan shiyyar, ta yadda za su jure kalubale da suka hada da yunwa, da rashin abinci mai gina jiki, da rikice-rikice da ma raba jama’a da muhallansu.

Rahoton ya kara da cewa, a shekarar 2020, mutane miliyan 54 ne, aka yi kiyasin sun fuskanci matsalar rashin abinci a shiyyar, kana daga cikin mafiya rauni da ka iya fuskantar yunwa da matsalar abinci mai gina jiki, har da mutane miliyan 8.9 da suka rasa matsugunansu, da wasu mutanen 4.7 da ke gudun hijira da masu neman mafaka.

A don haka, rahoton ya ba da shawarar samar da abinci a kan lokaci, da ruwan sha mai tsafta da muhimman magunguna ga al’ummomin da suka rasa muhallansu a babban yankin kahon Afirka, baya ga tabbatar da cewa, sun samu alluran riga kafin COVID-19, ta yadda za a kai ga magance matsalar jin kai. (Ibrahim)