logo

HAUSA

Saddam Muhammad Ishaq: Ina fatan daliban Najeriya za su samu damar karo ilimi a China!

2021-06-22 14:27:37 CRI

Saddam Muhammad Ishaq: Ina fatan daliban Najeriya za su samu damar karo ilimi a China!_fororder_微信图片_20210620165314

Saddam Muhammad Ishaq, wani dalibi dan asalin jihar Kanon tarayyar Najeriya ne, wanda a yanzu haka yake karatun neman digiri na biyu a jami’ar Chinese Academy of Sciences wato UCAS a takaice.

Saddam, wanda ya yi shekaru sama da biyu yana karatu a wannan makaranta dake birnin Beijing, ya ce fannin karatun da yake wato nazarin kwayoyin halittu, ko kuma cell-biology a turance, ya kunshi ilmomi da fasahohi na zamani da dama, wadanda ya dace a yi koyi daga kasar Sin, saboda zai kawo alfanu ga rayuwar dan Adam.

A ra’ayinsa, kasar Sin ta samu babban ci gaba a fannoni daban-daban, kuma hakan na da alaka sosai da jajircewa da dagewar da mutanen kasar suke yi.

A karshe, Saddam Muhammad Ishaq ya kuma yi kira ga matasan Najeriya, su tashi tsaye don karo ilimi. Musamman in suna da hali, ya kamata su zo nan kasar Sin don zurfafa karatunsu, da ganewa idanunsu ainihin halin da ake ciki a kasar.(Murtala Zhang)