logo

HAUSA

Wa yake keta hakkin dan Adam?

2021-06-21 15:53:53 CMG

Wa yake keta hakkin dan Adam?_fororder_hakki

Daga ranar 21 ga watan Yunin da muke ciki, an fara gudanar da taron majalisar hakkin dan Adam karo na 47 a kasar Switzerland, inda tun tuni kasar Amurka, da Canada, da Birtaniya, da wasu kasashe suka nuna cewa, za su gabatar da bayani dangane da yanayin hakkin dan Adam na jihar Xinjiang na kasar Sin, tare da yin suka kan kasar. Sun ce suna yin haka ne don “kare hakkin dan Adam”, amma a hakika suna keta hakkin dan Adam. Domin suna kokarin shafawa kasar Sin kashin kaza, gami da janyo hankalin jama’ar kasashe daban daban zuwa wani bangare na kuskure, inda ake suka kan wanda ba shi da laifi, yayin da wuraren da suke bukatar taimako suka zama wadan da ba a lura da su sosai ba.

Jihar Xinjiang wani wuri ne na musamman na kasar Sin, inda ake samun yaduwar ra’ayi na janyo wa kasa baraka, da ta’addanci, gami da ra’ayin kaifin kishin Islama. Bisa wadannan ra’ayoyi ne an wanke kwakwalwar wasu ‘yan kabilar Uygur na kasar Sin, har ma suna neman balle jihar Xinjiang daga kasar Sin, tare da kafa wata kasa ta kansu mai taken “Turkistan ta gabas”. Hakan ya yi kama da yadda wasu mutane suka nemi kafa kasar Biafra a kudancin kasar Najeriya a baya.

A lokaci daya, tunani na ta’addanci da kaifin kishin Islama sun shiga jihar Xinjiang, bi ta wasu kasashen dake yamma da kasar Sin, tare da haifar da mummunan tasiri kan wasu ‘yan Uygur, ta yadda suka fara neman balle jihar Xinjiang ta hanyar hare-haren ta’addanci. Abun da suke yi ya yi kama da yadda kungiyar Boko Haram ke neman kafa “kasar Islama” a arewacin Najeriya, ta hanyar hare-hare da kisan kiyashi.

Wannan yanayi ya sa gwamnatin kasar Sin ta karfafa matakan tsaro a jihar Xinjiang, tare da kafa wasu makarantun horar da fasahohin sana’a, don taimakawa kawar da tunanin janyo baraka da ta’adanci na wasu matasa, da koyar musu fasahohin da suke bukata don neman wani aikin yi. Bayan an yi wasu shekaru ana aiwatar da manufar, yanayin tsaro na jihar Xinjiang ya samu ci gaba sosai. Da ma an taba ganin abkuwar hare-haren ta’addanci fiye da dubu 1 a jihar Xinjiang, tun daga shekarun 1990. Amma tun daga shekarar 2016 har zuwa yanzu, ba a sake samun wani hari na ta’addanci a jihar Xinjiang ba. Sa’an nan, yanayi na tsaro da kwanciyar hankali ya ba da damar samun ci gaban tattalin arziki. A shekarar 2020, kowane mutum dake zama a jihar Xinjiang ya kan samu kudin shiga da ya kai dalar Amurka 3695, jimillar da ta karu da kashin 3.2% bisa shekarar 2019. Yayin da aka samu fid da mutane 3,064,900 da suke zama a cikin kauyukan jihar daga kangin talauci.

Sai dai ci gaban tattalin arzikin jihar Xinjiang, da yadda ake samun kwanciyar hankali, da kyautatuwar zaman rayuwar jama’a a wurin, ba wasu abubuwan da kasar Amurka, da wasu kasashe, za su lura da su ba. Kawai suna son amincewa da jita-jitar da wasu mutanen da suke neman janyo wa kasar Sin baraka suke yada. Abun da suke yi tamkar rubuta wani labari ne, inda da farko dai, za su tsara wani taken labari, wato “ gwamnatin kasar Sin na keta hakkin dan Adam a jihar Xinjiang”, daga baya za su yi amfani da karairayi da jita-jita a matsayin shaidu. Ba za su ji wuyar samun jita-jitar ba, saboda wadannan kasashen sun dade suna kokarin ta da rikici a jihar Xinjiang, ta hanyar ba da kudi ga mutanen da suke neman janyo wa kasar Sin baraka, da tallafawa wasu malamai masu nazarin al’amuran duniya wadanda ke daukar ra’ayin kin jinin kasar Sin. Wadannan mutane sun yi ta kokarin yada jita-jita dangane da jihar Xinjiang, da shafawa kasar Sin kashin kaza, ta hanyar wasu labaru da hotuna, gami da alkaluma marasa gaskiya.

Kasashen yamma sun ce suna “kare hakkin dan Adam”, amma a hakika suna fakewa da batun hakkin da Adam suna neman hana kasar Sin , wadda ke iya takara da su a kasuwannin duniya, samun ci gaba. Saboda haka, ko da yake gwamnatin kasar Sin na kokarin tabbatar da tsaro, amma sun ce gwamnatin na “Keta hakkin dan Adam”. Ko da yake kasar Sin tana kokarin hana yaduwar tunanin kaifin kishin Islama, amma hakan a ganin wasu kasashen yamma ya zama “cin zarafin Musulmai”. Ko da yake kasar Sin na gudanar da ayyukan noma bisa doka, amma sai a ce tana “tilastawa wasu mutane aiki”. Sa’an nan, yayin da jihar Xinjiang ke kokarin farfado da tattalin arzikinta daga mummunan tasirin da annobar cutar COVID-19 ta haifar, kasar Amurka da wasu kasashe suna kirayi ga kasashe daban daban domin su magance sayen auduga da sauran kayayyakin da ake samar da su a jihar Xinjiang. Hakan ya nuna cewa, sam wadannan kasashe ba su lura da moriyar jama’ar jihar Xinjiang ba.

Ban da wannan kuma, wani makasudi na kasashen yamma, shi ne neman karkata hankalin jama’ar kasashe daban daban zuwa ga batun hakkin dan Adam na kasar Sin, ta yadda ba za su lura da yadda su da kansu suke keta hakkin dan Adam ba: Misali, yadda ake tursasawa ‘yan asalin kasashen Afirka, da na Asiya a kasar Amurka, da yadda ake yawan yin amfani da bindigogi wajen kashe mutane a kasar, da tilastawa yara aiki a masana’antun hada taba, da yadda aka gano gawawwakin yara a cikin wata makarantar kasar Canada, da yadda ake nuna kyama da bambanci ga ‘yan wasu kabilu a kasar Birtaniya, ballantana kuma matsalolin da jama’ar kasashen da suka hada da Iraki, da Afghanistan, da Libya,da Sham suke fuskanta, sakamakon yake-yaken da kasashen yamma suka kaddamar, wadanda suka sanya kyawawan birane zama baraguzan gine-gine, da mai da gonar shinkafa ta zama gonar tabar wiwi, da tilastawa yara su zama sojoji, da mata su zama masu dauke da bom a jiki...

Hausawa su kan ce “ Munafuncin dodo ya kan ci mai shi.” A halin yanzu, tsarin duniya na sauyawa, kana sannu a hankali kasar Amurka da kasashen yammacin duniya sun fara rasa karfinsu na yin tasiri kan sauran kasashe. Wata rana za a tilasta musu biyan diyya ga kasashen da suka taba cin zarafinsu, gami da mutanen da suka keta hakkinsu. (Bello Wang)

Bello