logo

HAUSA

Xi Jinping da mahaifinsa: Yan JKS suna gadon hali na gari daga zuriya zuwa zuriya

2021-06-19 17:09:42 CRI

Xi Jinping da mahaifinsa: Yan JKS suna gadon hali na gari daga zuriya zuwa zuriya_fororder_xi-2

Ranar 20 ga watan Yuni, rana ce ta mahaifi, bari mu gaya muku wani labari game da mahaifi da dansa.

Xi Jinping da mahaifinsa Xi Zhongxun, dukkansu ‘yan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ne.

Xi Zhongxun yana ganin cewa, jami’an gwamnati da fararen hula sun kasance daidai wa daida ne, babu bambancin matsayin dake tsakaninsu, ya dace jami’an gwamnati su yi cudanya da fararen hula a ko da yaushe.

Xi Jinping da mahaifinsa: Yan JKS suna gadon hali na gari daga zuriya zuwa zuriya_fororder_xi-1

Xi Jinping shi ma yana nacewa kan manufar “bautawa jama’a” kamar yadda mahaifinsa Xi Zhongxun ya yi.

Kuma Xi Jinping ya koyi hali na gari na kwazo da himma da kuma saukin kai wato rashin bata abubuwa daga mahaifinsa, an gani a dakin karbar baki na Xi Zhongxun, babu na’urar talabijin, sai wasu tsoffin kujeru kawai. Wang Youhui, wanda ya taba yin aiki tare da Xi Jinping a gundumar Zhengding ta lardin Hebei ya taba ziyartar gidan Xi a shekarar 1983, daga baya ya bayyana cewa, “Na ga hali na gari na saukin kai wato rashin bata abubuwa a gidansa.”

Abin koyi kan kawo babban tasiri ga jama’a, kalaman da mahaifinsa ya yi da matakan da mahaifinsa ya dauka sun koyarwa Xi Jinping yadda zai zama wani mutum dake bautawa al’ummar kasarsa.(Jamila)