logo

HAUSA

Jami’in Zimbabwe: Babban ci gaban da kasar Sin ta samu ya bayyana nagartaccen shugabancin da JKS take da shi

2021-06-18 14:40:44 CRI

Bana shekara ce ta cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin. Wani babban jami’in jam’iyyar ZANU-PF ta Zimbabwe, wanda ya taba rike mukamin jakadan kasar Zimbabwe a nan kasar Sin, ya gaya wa wakiliyarmu cewa, bisa shugabancin JKS, kasar Sin ta samu babban ci gaba. Kuma kasashen Afirka ciki har da kasar Zimbabwe sun ci gajiyar ci gaban kasar Sin.

Jami’in Zimbabwe: Babban ci gaban da kasar Sin ta samu ya bayyana nagartaccen shugabancin da JKS take da shi_fororder_210618-rahoto-Sanusi Chen.JPG

Christopher Mutsvangwa, shi ne mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar ZANU-PF, kana sakatare mai kula da harkokin kimiyya a kwamitin kolin ZANU-PF, sannan shi ne shugaban kungiyar tsoffin sojoji masu ritaya, wadanda suka taba halartar yakin neman ’yancin kasar Zimbabwe. A tsakanin shekarar 2002 da ta 2006, ya zamo jakadan kasar Zimbabwe dake nan kasar Sin, sakamakon haka, ya ga yadda kasar Sin ta samu ci gaba da idanunsa.

Mr. Christopher Mutsvangwa ya ce, ci gaban da al’ummar Sinawa suka samu bisa jagorancin JKS ya kasance abun al’ajabi da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

A lokacin da na fara aiki a Beijing a shekarar 2002, na ga akwai wasu kekunan doki dake sayar da amfanin gona a gefen titi. Galibin gidajen kwana na fararen hula bene mai hawa daya ne kawai. Daga gidana dake da benaye 2 kadai, ina iya hangen nesa zuwa wasu kilomitoci. Na ga sauye-sauye da suka faru a gaban idona. Wasu manyan gine-gine masu benaye da yawa sun rika bullowa akai akai, sannan an daina ganin kekunan doki a kan titi, yayin da kuma motoci suka rika karuwa cikin sauri. A lokacin da na fara aiki a Beijing, babu layukan dogo na karkashin kasa da yawa. Mun taba kwashe sa’o’i uku a kan hanyarmu ta zuwa filin jirgin sama na Beijing, daga ofishin jakadancinmu dake Beijing. Amma yanzu cikin mintuna kimanin 20 kacal an isa filin jirgin . Lallai kasar Sin ta samu sauye-sauyen da ba a ga irinsu ba a tarihi.

Christopher Mutsvangwa ya nuna cewa, ci gaban da kasar Sin ta samu ya kasance kamar wani abin koyi ga sauran kasashen duniya, ciki har da kasashen Afirka. Kasar Sin ta bayar da babbar gudummawa ga kokarin bunkasa duk duniya baki daya.

“Kasar Sin ta samu babban ci gaba cikin gajeren lokaci, wannan ya kara wa kasashen Afirka kuzari da niyyar neman ci gaba. Ci gaban da kasar Sin ta samu bangare daya ne na ci gaban daukacin bil Adama baki daya. Bugu da kari, tunanin neman ci gaba da kasar Sin take da shi ya nunawa sauran kasashen duniya cewa, bai kamata a bunkasa tattalin arziki a wata kasa daya tilo ba, ya kamata ci gaban ya shafi dukkanin fadin duniya baki daya.”

Mr. Mutsvangwa ya bayyana cewa, bisa shugabancin JKS, kasar Sin ta yi shekaru da yawa tana kokarin neman hadin gwiwar kasashen Afirka, har ma ta taka muhimmiyar rawa, wanda ba a iya maye gurbinta ba wajen bunkasar kasashen Afirka. Mr. Christopher Mutsvangwa yana mai cewa, “Ba kamar yadda sauran kasashen duniya suke yi ba, a kullum kasar Sin na mai da hankali wajen ci gaban Afirka. Ta yi kokarin bunkasa dangantakar dake tsakaninta da Afirka, har ma ta kawo wa kasashen nahiyar fasahohin zamani da jari, ta yarda kasashen Afirka su ci gajiyar ci gaban da ta samu. A ’yan shekarun baya, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka ya kai sabon matsayi, karkashin inuwar dandalin tattaunawa na hadin gwiwar Sin da Afirka FOCAC, da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’. Kasar Sin ta yi kokarin taimakawa kasashen Afirka, wajen neman ci gaba, ta kuma bayyana wa duk duniya niyyarta, da matakanta na kokarin neman ci gaban daukacin bil Adama gaba daya.”

Sannan Mr. Mutsvangwa ya jaddada cewa, lokacin da take daidaita dangantakar dake tsakaninta da jam’iyyun siyasa na kasashen waje, jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS, ba ta bata tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashen duniya ba. Sakamakon haka, jam’iyyun siyasa na kasashen Afirka na girmama JKS kwarai. Mr. Christopher Mutsvangwa ya bayyana cewa, “Kasar Sin da kasashen Afirka, suna zama daidai wa daida. Kasar Sin ba ta taba tsoma baki cikin harkokin gidan kasashen Afirka ba. Kaza lika kasar Sin ta mutunta ka’idoji da tsare-tsaren siyasa wadanda sauran kasashen duniya ke bi. Wannan kuma shi ne dalilin da ya sa kasashen Afirka ke girmama JKS sosai.”

Mr. Christopher Mutsvangwa ya kara da cewa, ya gamsu da ci gaban da kasar Sin ta samu a fannonin tattalin arziki da zamantakewar al’umma da dai sauransu a kullum bisa jagorancin JKS. Kasar Sin tana kuma bayar da muhimmiyar gudummawarta, wajen tabbatar da zaman lafiya da ci gaban duk duniya baki daya. (Sanusi Chen)