logo

HAUSA

Daukacin bil Adama za su ci gajiya daga sabuwar tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin

2021-06-17 19:40:25 CRI

Daukacin bil Adama za su ci gajiya daga sabuwar tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin_fororder_shenzhou-12

Yau Alhamis 17 ga wata da safe da misalin karfe 9 ne, kasar Sin ta yi nasarar harba kumbon Shenzhou-12 dake dauke da ‘yan sama jannati guda uku zuwa sararin samaniya, wadannan ‘yan sama jannati za su kasance a tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin a karo na farko.

Jonathan McDowell, masanin binciken sararin samariya dake aiki a cibiyar nazarin yanayi da kadawar iska mai zafi ta Harvard-Smithsonian ya yi nuni da cewa, burin ‘yan sama jannati na kasar Sin shi ne gina sabon gidansu a sararin samaniya, ta yadda za a yi amfani da shi a nan gaba.

Sararin samariya dukiyar daukacin bil Adama ce, ya dace kasa da kasa su gudanar da hadin gwiwa a tsakaninsu yayin da suke kokarin binciken sararin samaniya, kawo yanzu kasar Sin tana yin hadin gwiwa da hukumar nazarin sararin samaniya ta MDD kan ayyukan gwaji guda 9 da kasashe 17 suka gabata, nan gaba kuma za a fitar da rahoton da abin ya shafa bisa mataki na biyu.

An lura cewa, kasar Sin ta dauki matakan ne domin gina tashar binciken sararin samaniya mallakinta, da ke zama wani dakin gwaji a sararin samaniya, inda daukacin bil Adama za su ci gajiya, kuma za a cimma burin yin kirkire-kirkire a fannonin kimiyyar sararin samaniya da rayuka da sauran fasahohin da abin ya shafa, ta yadda za ta taka rawa wajen binciken sararin samaniya da yin amfani da sararin samaniya cikin lumana.(Jamila)