logo

HAUSA

Harba kumbon Shenzhou-12 na kasar Sin ya karfafa fatan duniya na cin gajiya daga ci gaban kasar a fannin binciken samaniya

2021-06-17 16:46:55 CRI

Harba kumbon Shenzhou-12 na kasar Sin ya karfafa fatan duniya na cin gajiya daga ci gaban kasar a fannin binciken samaniya_fororder_1

Da safiyar ranar Alhamis 17 ga watan nan na Yuni ne, aka harba kumbon Shenzhou-12 mai dauke da ’yan sama jannatin kasar Sin 3, ta amfani da rokar Long March-2F, daga tashar harba taurarin dan adam ta Jiuquan, a Hamadar Gobi dake arewa maso yammacin kasar Sin.

Ko shakka babu, nasarar harba kumbon ta kara kafa wani sabon tarihi a fannin ci gaban da kasar Sin ke samu, game da binciken sararin samaniya, tare da burinta na kammala tashar binciken samaniya mallakin ta.

Duba da cewa, kasar Sin ta sha nanata burinta na amfani da fasahohin binciken sararin samaniya domin ayyuka na zaman lafiya, ta kuma sha mika goron gayyata ga sassan kasa da kasa da su shiga a dama da su, wajen tabbatar da cin gajiyar wannan cibiya, da ma sauran fasahohin binciken samaniya cikin hadin gwiwa, hakan ya nuna cewa nasarorin da Sin ke samu za su karfafa fatan daukacin al’ummun duniya, na cin gajiya daga wannan fanni.

Kasar Sin na kallon samaniya da duniyoyin da ta kunsa, a matsayin wata kaddara ta daukacin bil adama. Kaza lika Sinawa na fatan cin gajiya daga dukkanin nau’o’in binciken da take yi a duniyoyi daban daban, tare da sauran al’ummun duniya, ba tare da yin babakere ko yin mummunar takara da sauran sassa ba.

Harba kumbon Shenzhou-12 na kasar Sin ya karfafa fatan duniya na cin gajiya daga ci gaban kasar a fannin binciken samaniya_fororder_2

Kama daga binciken wata zuwa duniyar Mars, da kuma kumbunan da kasar ke harbawa marasa dauke da mutane, zuwa masu dauke da ’yan sama jannati, kasar Sin na kara zurfafa hadin gwiwa da sassa masu fatan ganin an cimma nasarori tare kamar kasar Rasha wadda ke matukar mara baya ga Sin a wannan fanni.

Wata shaida dake tabbatar da hakan ita ce, a shekarar 2019, Sin da MDD sun sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwar gudanar da wasu ayyuka a wannan fanni a mataki na kasa da kasa har guda 9. Wadannan ayyuka sun kunshi sassa 23 wadanda za su kunshi kasashe 17 don gudanar da bincike a fannin magunguna masu nasaba da sararin samaniya, da rayuwar dan adam a samaniya, da sauran muhimman fannoni na sama jannati, da sabbin fasahohi masu alfanu ga bil adama.

A wannan gaba da Sin ke daf da kammala gina sabuwar tashar samaniya domin cin gajiyar bil adama, kasar na fatan hakan zai dasa dan ba ga sabon fannin hadin gwiwar kyautata rayuwar bil adama, maimakon wata dama ta cimma riba da asarar wani bangare. (Saminu Hassan)