logo

HAUSA

Me kungiyar SCO ta kawo wa duniya a cikin shekaru 20 da suka gabata?

2021-06-16 10:42:12 CRI

Me kungiyar SCO ta kawo wa duniya a cikin shekaru 20 da suka gabata?_fororder_0616-01

Ranar 15 ga watan Yunin bana, rana ce ta cika shekaru 20 da kafuwar kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai wato SCO. Daga kungiyar da ke da kasashe membobi shida kacal a farkon kafuwarta, zuwa kungiyar da ke da kasashe membobi 8, da kasashe masu sa ido 4, da kuma kasashe masu yin shawarwari 6, kungiyar SCO ta tabbatar da zaman lafiya a yankin, tare da sa kaimi ga samun ci gaba a yankin, kana ta zama misali wajen tabbatar da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da kuma raya dangantakar demokuradiyya a tsakanin kasa da kasa.

A matsayin tsarin hadin gwiwa dake tsakanin kasashe mabambantan yanayi da tsarin siyasa, kungiyar SCO ta tabbatar da ruhin Shanghai, wato yin amana da juna da cimma moriyar juna, da zaman daidaito da yin shawarwari da juna, da girmama al’adu daban daban, da kuma samun bunkasuwa tare tun daga kafuwarta, wanda hakan ya kafa wani sabon tsarin hadin gwiwa a tsakanin kasashe da suka sha bamban wajen tsaruka da hanyoyin da suke bi, kuma an samu nasarori a fannoni daban daban.

Game da fannin yin hadin gwiwa wajen kiyaye tsaro, kasashe membobin kungiyar sun daddale jerin yarjejeniyoyin yaki da ta’addanci, tare da gudanar da atisayen soja na hadin gwiwa fiye da 10 ta fannin yaki da ta’addanci, wanda hakan ya tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Game da fannin hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya, a cikin shekaru 20 da suka gabata, yawan kudin harkokin shige da fice a tsakanin Sin da sauran kasashe mambobin kungiyar ya karu, daga dala biliyan 17.14 zuwa dala biliyan 244.85, adadin da ya karu da kashi 15 cikin dari a kowace shekara.

Abu mafi muhimmanci shi ne, kungiyar SCO tana tsayawa kan manufar ‘yan ba ruwanmu. Ta kuma yi kokarin sa kaimi ga raya odar kasa da kasa cikin adalci. Kana an kiyaye yin mu’amala da juna, da nuna goyon baya ga rawar MDD, da ra’ayin cudanyar bangarori daban daban, da kuma tabbatar da zaman lafiya da karko a duniya.

Wadannan abubuwa ne da tsarin kungiyar SCO ya kawo wa duniya a cikin shekaru 20 da suka gabata. (Zainab)