DAN DAMBEN NAJERIYA SULTAN ADEKOYA NA FATAN BUNKASA SANA’ARSA
2021-06-16 11:34:39 CRI
Wani matashin dan danben Boxing dake kudancin Najeriya mai suna Sultan Adekoya, ya bayyana aniyar bunkasa sana’arsa a nan gaba zuwa matakin kwararru.
Da farko, Sultan Adekoya wanda kan yi gudun motsa jiki a kewayen unguwar da yake, a yankin Egbeda na jihar Lagos, na bin sahun yara kanana da matasa masu motsa jiki a kullum, da nufin bunkasa damar su ta shiga damben Boxing a nan gaba.
Daya daga irin wadannan yara mai shekaru 12 na nuna dabarun wasan boxing, yana kokarin gina karfin damtsen sa, da kai naushi, da kare kai, tare da gwada motsa kafafu da ake bukata yayin wasan, inda kuma yake jiran umarni daga kocin sa Taiwo Adegbite, wanda ke gefe yana yiwa sauran masu yin horo da suka riga shi zuwa gyare gyare.
Adegbite, wanda aka fi sani da koci Tipo, ya bayyana matashi Adekoya a matsayin "Mai karfi da aiki tukuru " wanda kuma ke da matukar basirar damben boxing.
Wasu fayafayen bidiyo na Adekoya a lokacin da yake horo, wadanda aka yada a kafafen sada zamunta, sun ja hankalin masu sha’awar wasan, inda ministan wasanni da harkokin matasa Sunday Akin Dare, ya bayyana matashin a matsayin “Wanda zai zamo muhimmin tauraro a nan gaba".
Da yake karin haske game da makomar dan wasan, koci Tipo ya ce "Mutane sun san shi sosai. Yana da kwazo kwarai da gaske,". Mr. Adegbite wanda ke wannan tsokaci ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ya ce tuni Adekoya ya shiga wasannin dambe sama da 60, ciki har da na baje fasahohi da akan shirya, ya kuma samu manyan nasarori.
A shekarar 2016, an baiwa Adekoya kambin gasar hukumar shirya wasan dambe ta kasa da kasa wato WBC, bayan da aka amince ya kai matsayin dan wasa da ya nuna alamun zama tauraro na WBC, yayin wasan gabatar da ‘yan wasa masu hazaka da hukumar ta WBC ta shirya. ‘Yan wasan damben boxing a kalla 40 masu shekaru tsakanin shekaru 5 zuwa 16 sun halarci wasan, wanda ya gudana a Lagos.
Koci Adegbite ya kara da cewa, ya na da imini kan Adekoya, duba da yadda matashin ke ci gaba da inganta kwarewarsa, tun daga shekaru 7 da suka gabata ya zuwa yanzu. Ya ce "Sultan ya zo kofar gida na da kan sa, inda muke gudanar da horo. Yana tafiya ne kawai ya hange mu muna yin wasan. A lokacin bai wuce shekaru 5 ba. Sai kawai ya rugo ya dauki safar hannu na ta Boxing, ba tare da ya tambaye ni izini ba. Ya fara kaiwa mutane naushi”.
Kocin ya ce “Sai na cewa Adekoya ya zo da iyayen sa. Na kuma yi mamakin ganin su da sanyin safiyar washe gari. Sun amince dan su ya koyi damben boxing. Tun daga wannan lokaci ne kuma ya fara samun horo."
BURI DA FATAN NASARA
A wata zantawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Adekoya ya ce "Ina kaunar damben boxing. Ina fatan mayar da boxing sana’a ta". Adekoya ya ma ce gwanayensa a wasan, su ne shahararren dan damben Birtaniya wanda aka haifa a Najeriya wato Anthony Joshua, da kuma dan damben Amurka Floyd Mayweather.
Adekoya na zuwa yin horo tsakanin ranekun Litinin zuwa Juma’a, amma fa bayan ya je makaranta, sai kuma ranekun karshen mako da yake wuni yana yin horo, kana wasu lokutan ma yana halartar gasannin dambe da ake shiryawa.
An haifi Adekoya a unguwar Egbeda ta jihar Lagos, kuma a nan matashin ya rayu tare da iyayensa, da kuma kanwarsa. Dukkanin su na zaune ne a dakin haya tare da wasu iyalai 15 dake zaune a gida guda tare.
Da yake tsokaci kan nasarorin da dan sa ya samu, mahaifin sa Tosin Adekoya, ya ce "Sultan ya jawowa iyalin su farin jini. Ya ce “Mutane da dama kan nuna ni su ce kun gan shi: Shi ne mahaifin Sultan'" Tosin Adekoya wanda ya bayyanawa kafar Xinhua hakan, ya kuma nuna irin lambobin yabo da dan nasa ya lashe, cikin shekarun da ya yi yana wasan dambe, ciki har da kambin hukumar WBC.
Mr. Tosin Adekoya mai shekaru 40 da haihuwa, kuma kwararren bakaniken motoci, ya ce yana goyon bayan sana’ar da dan sa ya zabi yi dari bisa dari.
A cewar Koci Tipo, sana’ar damben boxing a Najeriya na biye da kwallon kafa wajen karbuwa, sai dai banbancin ta da kwallon kafa, wasan boxing a Najeriya dake yammacin Afirka, bai samu cikakkiyar bunkasa ba tukuna; don haka ba kasafai ‘yan wasan boxing masu tasowa ke samun tallafin da ya wajaba ba.
Ya ce duk da cewa akwai ‘yan Najeriya dake wasan boxing, kuma wadanda suka cimma manyan nasarori a gasannin shiyya, da na kasa da kasa, kalilan ne daga cikin su suka samu horo tare da kaiwa matsayin taurari duk a Najeriyar.
Wani kalubalen na daban dake addabar masu horas da ‘yan dambe, a cibiyoyi irin su “Tipo Boxing Academy”, wadda aka kafa shekaru kusan 9 da suka gabata, shi ne rashin managarcin dakin motsa jiki na zamani, mai kunshe da kayan motsa jiki da suka dace da ‘yan wasan dambe.
Koci Tipo ya ce yana gudanar da horas da ‘yan dambe ne kawai bisa sha’awarsa ga wasan, duba da cewa har yanzu, ba shi da wasu masu daukar nauyin aikin da yake yi, kuma suma wadanda yake horaswa ba su da kudin da za su iya biyan sa.
Ya ce "Idan na bukaci su biyani kudin horon da nake ba su, kuma ba su da shi, ke nan sai dai su bar basirar ta su a gida. Kuma wadannan yara kusan ko kudin cin abinci ma ba su da shi."
Koci Adegbite ya ce, akwai bukatar zuba jari mai tarin yawa a wasan boxing, a wannan gaba da ake fatan samar da ci gaba, da makoma mai kyau ga wasan Boxing a Najeriya.