logo

HAUSA

Yadda al’ummar Sinawa suke bikin Duanwu domin nuna kishin kasa da mutunta al’adu

2021-06-16 09:24:41 CRI

Bikin Duanwu na da dogon tarihi a nan kasar Sin, inda bisa tarihi ya nuna cewa, an kai shekaru kusan dubu biyu ana gudanar da wannan biki. A kan yi wannan biki ne, a ranar 5 ga watan biyar bisa kalandar gargajiya kasar Sin, kuma a wannan shekara bikin ya fado ne a ranar 14 ga watan Yuni wannan shekara

Yadda al’ummar Sinawa suke bikin Duanwu domin nuna kishin kasa da mutunta al’adu_fororder_20210616世界21022-hoto3

Ana kuma kiran bikin da sunaye daban-daban kamar bikin watan Mayu, ko bikin mawaka, ko bikin tseren kwale-kwale da sauransu.

A baya dai biki ne na Ibada, amma yanzu an fi danganta bikin da shahararren marubucin wake-waken nan mai suna Qu Yuan, wanda ya burge al’ummar kasar Sin matuka, game da yadda yake matukar kishin kasarsa da kuma wake-waken da ya rubuta, lamarin da jama’a su fi nuna kauna da kuma yarda da ra’ayin da ya gabatar game da asalin wannan biki.

An dai haifi Qu Yuan ne a shekarar 340 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihis Salam, a garin Zigui na yankin Danyang na daular Chu, wato garin Yichang na yanzu a lardin Hubei, kuma ya riga mu gidan gaskiya a shekarar 278 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihis Salam, kuma kakansa shi ne dan sarkin kasar Chu.

Qu Yuan ya taba zama jami’i a masarautar daular Chu, kuma ya yi biyayya sosai ga sarkin wancan daula, amma sauran jami’an fadar ba sa son sa. Wannan ne ma ya sa bayan mutuwar sarki, Qu Yuan ya yi gudun hijira, bayan da sabon sarkin daular da aka nada ya kore shi, bayan wasu da fadawa suka yi ta yada jita-jitar cewa, wai ya ci zarafin sarki. A karshe dai Qu Yuan ya kashe kansa a cikin kogi.

Yadda al’ummar Sinawa suke bikin Duanwu domin nuna kishin kasa da mutunta al’adu_fororder_20210616世界21022-hoto2

Daya daga cikin muhimman dalilan dake sa al’ummar Sinawa yin wannan biki, shi ne domin tunawa da marigayi Qu Yuan da kuma ra’ayinsa na kishin kasa, kuma za a fahimci hakan ta irin abubuwan da ake gudanarwa yayin wannan biki, ciki har da cin wani nau’in abinci da ake kira Zongzi, da tseren kwale-kwale.

Kuma a shekarar 1980, an sanya gasar tseren kwale-kwale cikin jerin wasannin motsa jiki na kasar Sin, inda a kowa ce shekara ake shirya gasa don lashe kofin Qu Yuan.

Ban da wannan, a yayin wannan bikin jama’a kan rataya ciyayi masu kamshi wadanda ke iya korar sauro da kwari da cututtuka a kofar shiga gida, tare da tsaftace dakunansu. Wannan nema ya sa a zamanin da, ake daukar bikin Daunwu a matsayin biki na kiwon lafiya, kuma a wannan rana jama’a kan tsaftace daki, da zuba ruwan da aka sanya maganin gargajiyar kasar Sin a cikinsa, da shan giyar da aka sanya maganin gargajiya, wadannan suna nuna kyawawan al’adun Sinawa.

A shekaru 10 da suka gabata, hukumar UNESCO, ta sanya bikin Daunwu na kasar Sin cikin jerin al’adun gargajiya na duniya, hakan ya sa bikin zama na farko cikin jerin bukukuwan gargajiya na kasar Sin da aka sanya a cikin jerin sunayen al’adun gargajiya. Duk da cewa, al’ummar Sinawa na gudanar da wannan biki ta hanyoyi daban-daban, amma ainihin ma’anar dake tattare da wannan biki ita ce, tunawa da dan kishin kasa Qu Yuan, abin da ya sa kishin ya zama jigon wannan biki na Quanwu. Kuma ana wannan biki ne a lokaci guda a fadin kasar Sin da ma inda Sinawa ke zaune. (Saminu, Ibrahim /Sanusi Chen)