logo

HAUSA

Kowa ya bar Gida, Gida ya bar shi

2021-06-16 16:35:29 CRI

Kowa ya bar Gida, Gida ya bar shi_fororder_微信图片_20210616163439

Al’ada wani muhimmin bangare ne na rayuwar kowace al’umma, kuma duk al’ummar da ta yi watsi da al’adarta, hakika wata rana za ta bace a doron kasa. Abinci, da sutura, da yanayin zaman iyali, tarbiya da bukukuwan al’adu, da makamantansu, na daga cikin abubuwan dake bayyana tsarin kowace al’umma.

Sinawa kamar sauran al’ummomi a duniya, na da nau’o’in abinci da suturun kabilu daban-daban dake zaune a sassan kasar, da ma bukukuwan al’adu.

Kamar bikin kalankuwa da tashe da kamun kifi da sharo da makamantansu a kasar Hausa, bikin Duanwu yana daya daga cikin muhimman bukukuwan gargajiyar kasar Sin, inda bayanai ke nuna cewa, an shafe kusan shekaru dubu biyu ana gudanar da wannan biki. A kan yi wannan biki ne, a ranar 5 ga watan biyar bisa kalandar gargajiya kasar Sin, kuma a wannan shekara bikin ya fado ne a ranar 14 ga watan Yuni.  

Ana kiran bikin na Duanwu da sunaye daban-daban, kamar bikin watan Mayu, ko bikin mawaka, ko bikin tseren kwale-kwale da sauransu. Tarihi ya nuna cewa, a baya biki ne na Ibada, amma yanzu an fi danganta bikin da shahararren marubucin wake-waken nan mai suna Qu Yuan, wanda ya burge al’ummar kasar Sin matuka, game da yadda yake matukar kishin kasarsa da kuma wake-waken da ya rubuta, lamarin da ya jama’a su fi nuna kauna da kuma yarda da ra’ayin da ya gabatar game da asalin wannan biki. Ban da wannan, a yayin wannan bikin jama’a kan rataya ciyayi masu kamshi wadanda ke iya korar sauro da kwari da cututtuka a kofar shiga gida, tare da tsaftace dakunansu.

Wannan ne ma ya sa a zamanin da, ake daukar bikin Duanwu a matsayin biki na kiwon lafiya, kuma a wannan rana jama’a kan tsaftace daki, da zuba ruwan da aka sanya maganin gargajiyar kasar Sin a cikinsa, da shan giyar da aka sanya maganin gargajiya, wadannan suna nuna kyawawan al’adun Sinawa.

An haifi Qu Yuan ne a shekarar 340 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihis Salam, kuma ya riga mu gidan gaskiya a shekarar 278 kafin haihuwar Annabi Isa Alaihis Salam, sannan kakansa shi ne dan sarkin kasar Chu. Marigayi Qu Yuan ya taba zama jami’i a masarautar daular Chu, kuma ya yi biyayya sosai ga sarkin wancan daula, amma sauran jami’an fadar ba sa son sa. Abin da malam Bahaushe ke cewa, ba a mugun Sarki sai mugun Bafade.

Wannan ne ma ya sa bayan mutuwar sarki, Qu Yuan ya yi gudun hijira, bayan da sabon sarkin daular da aka nada ya kore shi, bayan wasu da fadawa suka yi ta yada jita-jitar cewa, wai ya ci zarafin sarki. A karshe dai Qu Yuan ya kashe kansa a cikin kogin Miluo.

Daya daga cikin muhimman dalilan dake sa al’ummar Sinawa yin wannan biki, shi ne domin tunawa da marigayi Qu Yuan da kuma ra’ayinsa na kishin kasa, kuma za a fahimci hakan ta irin abubuwan da ake gudanarwa yayin wannan biki, ciki har da cin wani nau’in abinci da ake kira Zongzi, da tseren kwale-kwale.

Saboda muhimmancin wannan biki, a shekarar 1980, an sanya gasar tseren kwale-kwale cikin jerin wasannin motsa jiki na kasar Sin, inda a kowace shekara ake shirya gasa don lashe kofin Qu Yuan.

A shekaru 10 da suka gabata, hukumar UNESCO, ta sanya bikin Duanwu na kasar Sin cikin jerin al’adun gargajiya na duniya, hakan ya sa bikin zama na farko cikin jerin bukukuwan gargajiya na kasar Sin da aka sanya a cikin jerin sunayen al’adun gargajiya. Duk da cewa, al’ummar Sinawa na gudanar da wannan biki ta hanyoyi daban-daban, amma ainihin ma’anar dake tattare da wannan biki ita ce, tunawa da dan kishin kasa Qu Yuan, abin da ya sa kishin ya zama jigon wannan biki na Duanwu. Kuma ana wannan biki ne a lokaci guda a fadin kasar Sin da ma inda Sinawa ke zaune. Wannan ya nuna yadda al’ummar Sinawa ke martaba tare da kare bukukuwansu na gargajiya. Kayan Aro, ba ya rufe katara, kuma duk wanda ya bar gida, to gida ya bar shi. (Ibrahim Yaya)