logo

HAUSA

Rayuwar mazauna jihar Xinjiang ta inganta a sakamakon kyautatuwar muhallin halittun wurin

2021-06-15 15:29:44 CRI

A cikin ’yan shekarun baya, an dukufa kan kiyayewa da inganta muhallin halittu, a yayin da ake bunkasa tattalin arziki da zaman al’umma a jihar Xinjiang da ke arewa maso yammacin kasar Sin, kuma kwalliya ta biya kudin sabulu, ganin yadda aka samu gaggaruman nasarori. Abokiyar aikinmu Lubabatu na tare da karin haske.

A gundumar Qira da ke yankin Hotan na jihar Xinjiang, akwai fadin gonaki da aka shuka nau’o’in bishiyoyi da tsirrai da ke iya jure fari, ciki har da Branchy tamarisk da Cistanche, kuma mazauna wurin na musu ban ruwa.

Rayuwar mazauna jihar Xinjiang ta inganta a sakamakon kyautatuwar muhallin halittun wurin_fororder___172.100.100.3_temp_9500027_1_9500027_1_1_b298eb16-f167-40e8-9431-2066b3bb56e8

Sai dai sabanin yadda yanayin wurin ya kasance kore shar a yanzu, a baya wurin ya kasance hamada da ba a iya shuka komai a kan ta.

Gundumar Qira tana bangaren kudancin iyakar hamadar Taklamakan, har ma sama da rabin fadin gundumar ya kasance a cikin hamadar, a yayin da fadin dausayin da ’yan Adam ke iya rayuwa bai kai kaso 5% na fadin gundumar ba. A wannan wuri, ana fuskantar tsananin fari, baya kuma ga iska da rairayi, lamarin da har ya tilasta aka kaurar da gundumar har sau uku. Shugaban ofishin kula da aikin yaki da kwararowar hamada na hukumar kula da dazuzzuka da filin ciyayi ta gundumar ya tuna da cewa,“A shekarun 1970, rairayi ya mamaye wasu kauyuka 9, tare kuma da gonaki da fadinsu ya kai sama da kadada 1500, a sakamakon iska mai karfi da ya taso tare da rairayi, kuma wasu magidanta 63 ba yadda za su yi sai dai su yi kaura daga wurin, sakamakon yadda rairayi ya mamaye gonakinsu da gidajensu. ”

Don inganta muhallin wurin, daga shekarun 1970, an yi ta gudanar da aikin kare kwararowar hamada a gundumar Qira. Musamman ma tun bayan taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin da aka gudanar a shekarar 2012, an yi namijin kokari wajen dasa bishiyoyi da shuke-shuke don fatan ganin magance kwararowar hamada. Kwalliya ta biya kudin sabulu, yadda aka kai ga kare hamadar da ke da nisan kilomita 1.5 daga wajen gundumar zuwa sama da kilomita 12. Da ya tabo magana a kan zancen, shugaban ofishin kula da aikin yaki da kwararowar hamada na hukumar kula da dazuzzuka da filin ciyayi ta gundumar Qira ya yi alfahari da cewa,“Mun dasa bishiyoyi kimanin kadada dubu 16.7, a aikin da muke yi na yaki da kwararowar hamada, bishiyoyin da suka zamanto shingaye na kare kwararowar hamada.”

Bayan da aka magance matsalar kwararowar hamada kuma, an fara shuka nau’in tsirrai da ake kira Cistanche da ke iya rayuwa a cikin hamada, wanda kuma ya kasance magani mai daraja, don kara kudin shigar mazauna wurin. Ya zuwa yanzu, fadin gonakin Cistanche da ake nomawa ya kai kimanin kadada 2800, wadanda ke samar da Cistanche da kudinsu ya kai sama da yuan miliyan 55 a kowace shekara. Lalle muhallin halittu da ya inganta cikin hamada, ya zama tushen tattalin arziki ga mazauna wurin.

Rayuwar mazauna jihar Xinjiang ta inganta a sakamakon kyautatuwar muhallin halittun wurin_fororder___172.100.100.3_temp_9500027_1_9500027_1_1_63a26604-bfbc-48b8-9134-3abaece61a6b

Sai kuma a yankin kudancin jihar Xinjiang da ake fuskantar fari da karancin ruwan sama, an kuma kara karfin kiyaye fadamu da suke da daraja sosai a wurin, inda aka gabatar da matakai da dama na inganta, matakan da suka kare yanayin fadamun, tare kuma da inganta muhallin rayuwar mazauna wurin.

A wurin shakatawa na fadamun tabkin Beihu da ke birnin Kashgar, mazauna wurin suna yawo da ma motsa jiki, a yayin da agwagi ke kiwo a tabkin. Tabkin yana arewa maso yammacin birnin na Kashgar, sai dai a sabanin kyakkyawan yanayi na yanzu, a baya ruwa mai wari, da ma tarin shara ne kadai ake gani a wurin. Ya zuwa shekarar 2017, bisa ga nazari da ma shawarwari da aka yi, gwamnatin birnin ya tsai da kudurin gina wurin shakatawa a wajen, don a gyara muhallin halittu na wurin, tare kuma da kyautata rayuwar mazauna birnin. Wani mazauniyar birnin ta shaida mana cewa,“A baya cin kasuwa ne kadai muke yi, sabo da babu wurin da muke iya zuwa shakatawa. Amma yanzu muna iya zuwa tabkin Beihu da ma kogin Tuman. Wadanda ke son motsa jiki suna zuwa wajen a kowace rana, gaskiya abu ne mai kyau sosai.”