logo

HAUSA

Kaddamar Da Layin Dogon Lagos Ibadan Ya Kara Alamta Sahihiyar Aminantaka Sin Da Najeriya

2021-06-14 17:52:28 CRI

Kaddamar Da Layin Dogon Lagos Ibadan Ya Kara Alamta Sahihiyar Aminantaka Sin Da Najeriya_fororder_210614-sharhi-Ahmad-hoto1

Masu hikimar magana da na cewa, “kowace kwarya da abokiyar burminta.” Har kullum jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta sha nanata aniyyarta na neman karfafa alaka gami da cudanya da kasashe masu tasowa musamman nahiyar Afrika. Ko shakka babu, dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika tana ci gaba da kyautata, kuma ana kara samun kulla alaka tsakanin bangarorin biyu musamman a fannonin ciniki, da tattalin arziki, da harkokin diflomasiyya, da hadin gwiwar ayyukan samar da muhimman kayayyakin more rayuwa. Kasar Najeriya ta kasance a matsayin daya daga cikin manyan aminan kasar Sin daga yammacin Afrika. Idan za mu iya tunawa a ranar 10 ga watan Fabrairun wannan shekarar aka gudanar da murnar cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Najeriya, a lokacin bikin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya taya takwaransa na Najeriya murnar cikar kasashen shekaru 50 da kafuwar huldar diflomasiyya, inda a nasa bangaren, shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, ya yabawa kasar Sin bisa yadda take tallafawa Najeriya a fannoni daban-daban kamar fannonin raya filayen jiragen sama, da samar da hasken lantarki, da ayyukan gina layin dogo da makamantansu. Hakika, kwalliya tana biyan kudin sabulu game da alakar Sin da Najeriya, alal misali, a karshen wannan makon ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya kaddamar da layin dogo da ya hada biranen Lagos da Ibadan dake yankin kudu maso yammacin kasar a hukumance, a wani mataki na saukaka zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a kasar dake yammacin Afirka. A jawabinsa yayin bikin kaddamar da titin, wanda ya gudana a tashar jirgin kasa ta Mobolaji Johnson dake Lagos, shugaba Buhari ya bayyana kammala aikin, a matsayin wani zakaran gwajin dafi a kokarin da gwamnati ke yi na farfado da tsarin sufurin jirgin kasa a Najeriya. Shugaba Buhari ya kara da cewa, fara aiki da titin, wanda kamfanin CCECC na kasar Sin ya gina, zai sanya titin jirgin kasa a Najeriya zama wani zabi na sufurin fasinjoji da ma kayayyaki.

Kaddamar Da Layin Dogon Lagos Ibadan Ya Kara Alamta Sahihiyar Aminantaka Sin Da Najeriya_fororder_210614-sharhi-Ahmad-hoto2

A nasa jawabin, jakadan kasar Sin a Najeriya Cui Jianchun, ya bayyana cewa, baya ga sufurin jama’a da kayayyaki, layin dogo tsakanin Lagos-Ibadan zai kuma saukaka harkokin kasuwanci, da ma inganta rayuwar al’ummar kasar. Yana mai cewa, bikin kaddamar da titin, ba kawai ya nuna irin goyon bayan da kasar Sin take bayarwa wajen bunkasa tattalin arziki da jin dadin jama’ar Najeriya bane, har ma ya kasance wata alama, ta hangen nesa kan shawarar gwamnatin Najeriya. Ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba sahihiyar manufa da kyakkyawan sakamako da aminci na yin aiki da Najeriya, don magance kalubale, har a kai ga gina shawarar Ziri daya da hanya daya tare. Ko shakka babu, dangantakar Sin da Najeriya tana kara kyautata, kuma ana fatan alummomin kasashen biyu zasu cigaba da cin moriyar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu nan da wasu shekaru aruru.(Ahmad Fagam)