logo

HAUSA

JKS tana kokarin cika alkawarinta na samun wadata ta bai daya a kasar Sin

2021-06-14 20:37:06 CMG

JKS tana kokarin cika alkawarinta na samun wadata ta bai daya a kasar Sin_fororder_20210614-sharhi-Bello

Tun fil azal, Sinawa suna da burin gina kasa mai wadata ta bai daya tsakanin al’ummominta. Yanzu sun fara ganin yiwuwar cika wannan burin. A kwanakin baya, kasar Sin ta gabatar da shirinta na kafa wani yankin samun wadatar bai daya na gwaji, a lardin Zhejiang dake gabashin kasar. Wannan batu ya nuna cewa, bayan da kasar ta yi nasarar cimma burin kawar da talauci a bara, yanzu ta kama hanyar kokarin cimma burin samun wadatar bai daya tsakanin al’ummunta.

An fitar da ra'ayi na samun wadatar bai daya tun kafin tasowar tattalin arzikin kasar Sin. A shekarar 1979, tsohon jagoran kasar, Deng Xiaoping, ya yi nazari kan wasu matsalolin da aka fuskanta bayan kafuwar sabuwar kasar Sin a shekarar 1949, daga baya ya ce “Kokarin magance bambanci a fannin ci gaban tattalin arziki ba zai haifar da alfanu ba”. A ganinsa, dole a bar wasu yankuna, wadanda suke da hali, su samu ci gaban tattalin arziki kafin wasu. Daga baya yankunan da suka samu wadata za su taimaki wuraren da suke da koma bayan tattalin arziki. A karshe kowa zai samu wadata. A lokaci guda, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje, inda wasu yankunan dake gabashin kasar, wadanda suke dab da bakin teku, suka samu ci gaban tattalin arziki cikin sauri, ta hanyar raya masana’antu, da cinikayya da kasashen waje. Daga bisani, jari da fasahohin da aka samu a wadannan wurare, su ma sun yi tasiri kan yankunan dake tsakiya da yammacin kasar Sin, tare da haifar da ci gaba.

Yanzu aikin da ya rage, shi ne kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki na bai daya. Hakan ya dace da tsarin siyasa na gurguzun da ake bi a kasar ta Sin.

Abin tambaya a nan shi ne, me ya sa aka zabi lardin Zhejiang don gina yankin samun wadatar bai daya na gwaji? Da farko dai saboda ci gaban tattalin arzikin lardin, inda yawan kudin shiga na jama’ar lardin ya dade a kan gaba a cikin dukkan lardunan kasar. Na biyu, ana samun daidaiton ci gaban tattalin arzikin birane da na kauyuka a lardin. Kana na uku, akwai kamfanoni masu zaman kansu da yawa a Zhejiang, wadanda suke samar da dimbin guraben aikin yi, da baiwa gwamnati damar ware karin kudi ga bangaren samar da hidimomi. Sa’an nan, na hudu, mutanen Zhejiang sun saba da sabbin manufofi, domin a kan gwada wasu manufofi a wurin, kafin a yayata su zuwa wurare daban daban.

A watan da ya gabata, na ziyarci gundumar Chun’an dake lardin Zhejiang. Wuri ne mai kyakkyawan muhalli. Ci gaban tattalin arzikin kauyukan gundumar ya sa mutane fara sanin muhimmancin muhallin halittu. Maimakon gurbata muhalli, sun yi kokairn kare ruwa, da itatuwa, ta yadda amfanin gona da suke samarwa, da otel-otel da suka kafa, za su kara yin daraja.

A gundunmar Chun’an dake lardin Zhejiang, kowane kauye na kokarin raya wasu sana’o’i, bisa yanayin da kauyen ke ciki. Misali, a gina kananan otel-otel da raya aikin yawon shakatawa a wurin da ake samun kyan muhalli. Kana a wurin da ke da magungunan gargajiya, sai a kafa masana’antu don sarrafa su. A kauyen da aka fi gudanar da aikin gona, sai a yi amfani da dabarar inganta amfanin gonan da ake samarwa, ta yadda za su kara samun karbuwa a kasuwa. Yayin da ake gudanar da wadannan ayyuka, su kuma jami’an gwamnati sun samar da gudunmowa sosai a kokarin raya sana’o’i na msuamman. Tamkar manyan ‘yan kasuwa masu kamfanoni, wadannan jami’ai sun san yanayin da kauyukan suke ciki sosai. Kana kullum suna kokarin gwajin wasu dabaru na raya masana’antu, da tallata kayayyaki, gami da baiwa jama’a damar samun karin kudin shiga.

A lokacin da na wuce lardin Zhejiang, na ga wasu mazauna kauyuka sun gina manyan gine-gine masu kyan gani, inda suke zama a ciki. Abun ya ba ni mamaki sosai kan yadda manoman suke da wadata. Daga baya, bayan da na ga alkaluman tattalin arzikin lardin, na yi mamaki sosai kan yadda ake samun daidaito tsakanin tattalin arzikin birane da na kauyukan lardin. Sa’an nan na ziyarci wasu kauyukan lardin, inda na gudanar da bincike cikin tsanaki, da fara fahimtar dalilin da ya sa wadannan kauyuka ke samun wadata. Wannan dalilin shi ne, tunanin mutum ya sauya, tare da samun ci gaba. Mutanen wadannan kauyukan, wasun su sun taba karatu da zama a manyan birane, yayin da wasu sun dade suna kula da kamfanoni na kansu. Kana wasu na kokarin gwajin wasu sabbin fasahohi, karkashin jagorancin jami’ai, da malamai masu ilimi. Bayan tunanin mutum ya sauya sosai, mutane su kan iya samun wata dabara mai inganci, wadda ta dace da yanayin da suke ciki, a kokarin raya kansu.

Sabuwar manufar da aka gabatar a wannan karo ta kayyade cewa, za a cimma burin samun wadatar bai daya a shekarar 2035, a lardin Zhejiang na kasar Sin, inda dukkan fannoni masu alaka da siyasa, da al’adu, da muhallin halittu, dukkan su za su samu ci gaba sosai. Daga bisani, kasar Sin za ta samu wasu fasahohi na wanzar da wadatar bai daya, wadanda za ta raba su ga sauran yankunan kasar, gami da duniya baki daya.

Ban da wannan kuma, sabuwar manufar ta nuna kokarin da jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin take a fannin cika alkawarin da ta dauka. Da ma jam’iyya mai mulki a kasar Sin ta yi alkawari kawar da talauci gaba daya daga kasar, sa’an nan ta yi nasarar cika wannan alkawari a shekarar 2020. Zuwa yanzu, tana kokarin neman cika alkawarinta na samun wadatar bai daya tsakanin al’ummar kasar. Hausawa su kan ce, “Kyan alkawarin cikawa.” A nan kasar Sin, muna ganin yadda gwamnati da jama’ar kasar suke kokarin aiwatar da shirin da aka tsara, da cika alkawarin da aka dauka, ta yadda sannu a hankali ake kokarin raya kasar don zama kasa mai cikakken ci gaba. (Bello Wang)

Bello