logo

HAUSA

Za a dakatar da matakin kulle da aka sanya a wasu yankunan birnin Guangzhou bisa matakai daban daban

2021-06-14 16:08:17 CRI

Yau Litinin cibiyar ba da jagoranci kan aikin dakile cutar COVID-19 ta birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin ta fitar da sanarwa cewa, domin kara kyautata aikin kandagarkin cutar, birnin zai soke matakin kulle a wasu yankunan da aka rufe bisa matakai daban daban.

Idan yankunan da aka rufe sun dace da sharuda kamar su: babu sabon wanda ya harbu da cutar bayan da aka yi wa daukacin mazauna yankin gwajin kwayar cuta sau uku a cikin kwanaki 14 da suka gabata, ko kuma an kebe daukacin mutanen da suka yi cudanya da masu harbuwa da cutar, ko kuma an tabbatar da lafiyar daukacin mutanen da suka taba zuwa wurin da mai harbuwa da cutar ya taba sauka, ban da haka ya dace a tabbatar da cewa, babu kwayar cutar a wadannan yankunan.(Jamila)