logo

HAUSA

Bayani game da bikin Duanwu na kasar Sin

2021-06-14 16:14:19 CMG

Bayani game da bikin Duanwu na kasar Sin_fororder_微信图片_20210614161150

Bikin Duanwu, ko Dragon Boat Festival, biki ne dake gudana a duk ranar 5 ga watan 5 bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wanda a bana ya fado a yau Litinin 14 ga watan Yuni. Manufar bikin ita ce, tunawa da dan kishin kasa kuma fitaccen marubucin wakoki na kasar, Qu Yuan, wanda ya tsunduma kansa cikin kogin Milou don sadaukar da ransa da nufin wanke kansa daga zargi. Kana al’umma na amfani da wannan rana domin  gudanar da wasu al’adu da nufin kawar da duk wani sharri da kuma fatan samun alkhairi. (Faeza)

Faeza