logo

HAUSA

Sharhi: Yadda Twitter ke nuna fuska biyu ya sake nuna wa duniya ainihin ma’anar ‘yanci da dimokuradiyya a bakin wasu kasashen yamma

2021-06-13 22:00:40 CRI

Sharhi: Yadda Twitter ke nuna fuska biyu ya sake nuna wa duniya ainihin ma’anar ‘yanci da dimokuradiyya a bakin wasu kasashen yamma_fororder_微信图片_20210613215429

Kwanan nan, yadda gwamnatin Nijeriya ta dakatar da ayyukan shafin sada zumunta na Twitter ya jawo hankalin kasa da kasa, har ma Amurka da Burtaniya da ma tarayyar Turai suka fitar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka zargi gwamnatin Nijeriya da keta hakkin bil Adam da ma ‘yancin jawabi, lamarin da ya sake shaida yadda Amurka da kasashen yammaci suka nuna fuska biyu da kuma ma’anar ‘yanci da dimokuradiyya a bakinsu.

Lalle lamarin ya faru ne a sakamakon yadda kafar Twitter ya goge wani sakon da shugaban Nijeriya Mohammadu Buhari ya wallafa ta kafar,inda ya gargadi masu tada rikici a kasar. A sakon da aka goge, shugaban ya bada misali da yakin basasar da ya shafe watanni 30 a kasar tsakanin 1967 zuwa 1970, yana mai gargadin wadanda suke son ganin gwamnatin ta gaza, da su kaucewa tada fitina. Twitter ya goge sakon shugaban bayan wasu masu amfani da shafin sun yi ta sukarsa.

Sai dai a cewar kafofin yada labarai na Nijeriya, yadda kafar Twitter ta goge sakon shugaban na daya ne daga cikin dalilan da suka sa gwamnatin kasar ta dakatar da ayyukan Twitter din. A hakika a zanga-zangar End SARS da aka gudanar a shekarar 2020, kafar Twitter ta taka muhimmiyar rawa, inda ta samar da sauki ga masu zanga-zanga.

Bayan da Twitter ya goge sakon shugaba Buhari, ministan yada labarai da raya al’adu na kasar Lai Mohammed ya zargi Twitter da nuna fuska biyu, tare da nuna shakku game da ka’idojin Twitter.Yana mai cewa, “mai yuwuwa Twitter na da nasa ka’idoji, amma kuma ba ka’idoji ne na bai daya ba. Idan shugaban kasa, a ko ina a duniya, ya damu da wani yanayi, yana da‘yancin bayyana ra’ayinsa,” yana mai cewa, amma shafin bai dauki wani mataki kan sakonnin da jagororin ‘yan aware a Nijeriya suke wallafawa ba. Ya kara da cewa, a lokacin da mutane suke kona ofisoshin ‘yan sanda tare da kashe su yayin zanga-zangar End SARS, a ganin Twitter, suna da ‘yancin gudanar da zanga-zanga. Amma a lokacin da makamancin lamarin ya faru a Amurka, sai ya zama tawaye.

Abin haka yake, kuma a hakika kafofin yada labarai na Amurka da ma kasashen yammacin duniya sun saba da nuna fuska biyu, kuma wannan ba shi ne karo na farko da Twitter ya yi haka ba.

Yayin da aka samu matsalar gyara doka a yankin Hong Kong a shekarar 2019, shahararrun kafofin sada zumunta na kasar Amurka kamar su Twitter da Facebook da sauransu sun taba dakatar da shafukan masu amfani da kafar sama da dubu daya bisa dalilin wai suna ba da labaran karya ko suna samun goyon bayan gwamnatin kasar Sin, amma hakika kafofin sun gabatar da labarai na hakika da suka faru a yankin Hong Kong. A sa’i daya kuma, kafar Twitter ba ta kula da sakwannin da suke shafa wa ‘yan sandan Hong Kong da gwamnatin kasar Sin bakin fenti ba.

Ranar 13 ga watan Disamban bara, rana ce ta bakwai ta nuna juyayi ga wadanda suka rasu yayin kisan gillar da aka yi a birnin Nanjing, inda daukacin al’ummun kasar Sin suka yi bakin ciki matuka ga ‘yan uwansu sama da dubu 300 wadanda suka mutu sakamakon kashe-kashen da maharan Japanawa suka yi musu, tare kuma da nuna fatansu na koyon darasi daga tarihi da darajanta zaman lafiya, amma kowa ya ga abun bacin rai da ya faru a kafar Twitter, inda aka goge hotunan tarihi da hoton bidiyon kisan gillar da ya faru a Nanjing da wasu masu shiga dandalin suka yi, bisa dalilin hotuna marasa dadin gani, a yayin da kuma suka bari sakwannin da masu tsattsauran ra’ayi na Japan suka wallafa su yadu ta kafar wadanda suka gurbata ainihin gaskiyar abin da ya faru a tarihi. Kamar yadda aka sani, kisan gillar Nanjing da ya faru a shekarar 1937 laifi ne da kotun sojan kasa da kasa mai kula da yankin gabashin Asiya ta tabbatar, hotuna da kafar Twitter ta goge hotuna ne da suka shaida abubuwan da suka faru a tarihi, wadanda suka samu amincewa daga al’ummun kasa da kasa,

Irin wannan abubuwa ba sa lisaftuwa. Matsayin da Twitter ya dauka ya dogara ne ga rukunonin da ke mara mata baya, kuma moriyar kasar Amurka ce kafar Twitter take wa aiki, a maimakon a ce ita kamfani ce mai zaman kansa. Yadda kafar Twitter ke nuna fuska biyu, ya sake nuna ainihin ma’anar ‘yanci da dimokuradiyya a bakin kasashen yamma.  (Lubabatu)