logo

HAUSA

Tilas ne Amurka da yankin Taiwan su dakatar da aikin neman ’yancin kan Taiwan ta fakewa da yaki da cutar COVID-19

2021-06-12 20:30:38 CRI

Tilas ne Amurka da yankin Taiwan su dakatar da aikin neman ’yancin kan Taiwan ta fakewa da yaki da cutar COVID-19_fororder_0612-1

Bayan da jami’ai uku na majalisar dokokin dattijai ta kasar Amurka suka dauki jirgin saman soja na dakon kayayyaki suka kai ziyara yankin Taiwan bisa hujjar samarwa yankin Taiwan alluran rigakafin cutar COVID-19, jami’an majalisar dokokin dattijai ta kasar Amurka guda biyu daban, wato Edward Markey, da Mitt Romney, sun bayar da sanarwa a kwanakin baya cewa, za a gudanar da taron sauraron ra’ayoyi game da yadda za a inganta dangantakar dake tsakanin Amurka da yankin Taiwan, sun kuma yi kira da a biya karin bukatun yankin Taiwan, wato kara samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 ga sojojin yankin da sauransu.

Ya zuwa yanzu, kowa ya sani, aikin yaki da cutar COVID-19 da Amurka da yankin Taiwan suka gudanar, aiki ne neman ’yancin kan Taiwan a yankin. Kaza lika jama’ar yankin Taiwan ba su yi imanin Amurka za ta taimake su wajen kawar da yanayin yaduwar cutar COVID-19 ba.

Amma bayan da yanayin samun yaduwar cutar COVID-19 a yankin Taiwan ya tsananta, tun daga farkon watan Mayu, babban yankin kasar Sin ya bayyana cewa, zai yi kokarin taimakawa jama’ar yankin wajen samun alluran rigakafin cutar.

Batun yankin Taiwan yana shafar babbar moriyar kasar Sin, kana batu ne mafi muhimmanci a fannin raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. Kuma Sin ba ta amince da duk wani mutum, ko wani bangare ya saba wa manufar kasancewar Sin daya tak a duniya ba. Kuma Sin za ta mayar da martani kan duk wanda ya ci gaba da aiwatar da matakan balle yankin Taiwan daga kasar Sin. Don haka game da wannan, bai kamata Amurka ta tsaida kuduri maras dacewa ba. (Zainab)