Kasuwar motocin hakar kasa ta Sin ta bunkasa cikin watanni 5
2021-06-12 16:34:52 CRI
Wasu alkaluma da kungiyar makera kayan gine-gine ta kasar Sn ta fitar sun nuna cewa, kasuwar motocin hakar kasa ta Sin, ta bunkasa cikin watanni 5 da suka gabata.
Rahotanni sun nuna cewa, kamfanonin dake kera irin wadannan motoci dake Sin, sun sayar da motocin 200,733 tsakanin watan Janairu zuwa Mayu, karuwar da ta kai ta kaso 37.7 bisa dari a shekara guda.
Kaza lika alkaluman sun nuna cewa, cikin wadannan watanni 5, motocin na hakar kasa da aka samar a kasuwannin cikin kasar, sun kai 176,735, karuwar da ta kai ta kaso 31.7 bisa dari, sama da na makamancin lokaci a bara, yayin da yawan wadanda aka fitar zuwa ketare suka kai 23,998, wato karuwar kaso 106.3 bisa dari, sama da na shekarar da ta gabata.
A watan Mayu kadai, adadin irin wadannan motoci da kamfanonin Sin suka sayar sun kai 27,220, adadin da ya yi kasa da na makamancin lokaci a bara da kaso 14.3 bisa dari. (Saminu)