logo

HAUSA

Kasar Sin ta kafa dokar yaki da ra’ayin nuna isa da wasu kasashen yamma ke nunawa a duniya

2021-06-11 11:22:16 CRI

A jiya ne a yayin wani taron zaunnnen kwamitin majalisar kafa dokokin kasar Sin, an zartas da “Dokar Dakile Tukunkumin Da Kasashen Waje Suka Sanya”. Wannan dokar da kasar Sin ta kafa, tamkar kara wani “kayan aiki” kan matakan da take dauka na nuna adawa da takunkumi da tsoma baki da karfin kotu na hukunta wani a wata kasa, ta yadda kasar Sin za ta iya kara tsaron ikon mulkin kanta da tsaron kai da moriyarta da ta samu bayan na samu ci gaba, har ma za ta iya kara tabbatar da adalci da zaman daidai wa daida tsakanin kasa da kasa.

Kasar Sin ta kafa dokar yaki da ra’ayin nuna isa da wasu kasashen yamma ke nunawa a duniya_fororder_210611-bayani-Sanusi Chen

Hausawa kan ce “ka yi min ni ma na mayar maka da martani”, wannan ne dalilin da ya sa kasar Sin ta kafa wannan doka. A ’yan shekarun baya, wasu kasashen yamma sun kirkiro wasu karairayi game da yankunan Xinjiang da Hongkong na kasar Sin, inda suka sanya takunkumi kan wasu hukumomi da wasu ma’aikata na kasar Sin, da nufin cimma burinsu na dakatar da ci gaban kasar Sin. Irin wannan karfin kotu na hukunta wani a wata kasa, ya keta akidar dokokin kasa da kasa, da dangantakar dake tsakanin kasa da kasa, amma wadannan kasashen yamma har yanzu suke amfani da shi, kuma hakan tsoma baki ne kan harkokin cikin gidan kasar Sin, wanda kuma zai kawo illa sosai ga tsare-tsaren kasa da kasa, musamman majalisar dinkin duniya, MDD.

Irin wadannan takunkuman da wasu kasashen yamma suke sanya mata a kullum, ya zama wajibi ga bangaren Sin ya kafa doka, ta yadda zai mayar da martani a kan lokaci. Ba ma kawai yana son tsaron mutuncinsa da moriyarsa mafi muhimmanci ba, har ma yana namijin kokarin kare ka’idojin nuna adawa da tsoma baki kan harkokin gidan wani da zaman daidai wa daida tsakanin kasa da kasa, sannan yana kokarin yakar mulkin danniya da siyasa irin ta masu fada a ji. Sabo da haka, ana iya ganin cewa, kasar Sin tana nuna adalci a lokacin da ta kafa “Dokar Dakile Tukunkumin Da Kasashen Waje Suka Sanya” bisa dokokin kasa da kasa. Ba kamar yadda wasu kasashen yamma, musamman kasar Amurka su kan dauki matakan mulkin danniya kan sauran kasashen duniya ba.

Bisa sunan wannan doka, ana iya ganin cewa, tana “nuna adawa” ne kawai, wato, kasar Sin ba za ta riga sauran kasashe daukar matakan sanya tukunkumi kan wata ko wani ba. Wannan ya kuma bayyana cewa, kasar Sin za ta ce “A’a” da kuma daukar matakan dakile duk wani irin nau’in sanya takunkumi da wasu kasashen yamma su kan dauka kamar yadda su kadai suke so. Jaridar “Independent” ta kasar Rasha ta nuna cewa, wannan doka, za ta kasance kamar wani tubalin doka a lokacin da gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan dakile matsin lamba da kasar Amurka da kawayenta suka yi mata.

Kasar Sin ta kafa dokar yaki da ra’ayin nuna isa da wasu kasashen yamma ke nunawa a duniya_fororder_210611-bayani-Sanusi Chen2

A hakika dai, a lokacin da kasar Sin ta kafa wannan doka, ta yi koyi da dabaru na sauran kasashen duniya. Alal misali, a shekarar 1996, kungiyar kasashen Turai, wato EU ta kafa dokar "EU Blocking Act" domin dakile takunkumin da kasar Amurka ta kan sanya mata. Bisa wannan dokar EU, idan takunkumin da kasar Amurka ta kakabawa wata kasa ta daban, ya kawo illa ga kamfanoni da masana’antun mambobi kasashen EU, wadannan kamfanoni da masana’antun EU, ba su bukatar martaba tanade-tanaden dake cikin takunkumin da kasar Amurka ta sanya ba, har ma za su iya neman kudin fansa ko diyya daga kasar Amurka. Bugu da kari, a watan Yunin shekarar 2018 ma, kasar Rasha ta fitar da wata dokar dakile takunkumin da aka sanya mata, domin kare moriyar kasar Rasha da al’ummarta.

Kasar Sin ta kafa wannan doka domin mayar da martani ga takunkumin da aka sanya mata, ta hanyar tsoma baki a harkokin cikin gidan ta, da bata sunan kasar Sin da kuma keta halaltaccen iko na wasu masana’antu da daidaikun al’ummar Sinawa, ta yadda ba zai yi tasiri ga masana’antu da daidaikun mutane wadanda suke tafiyar da harkokinsu a kasar Sin bisa doka ba. Tabbas, babu wanda zai iya canja niyyar kasar Sin ko kadan ta manufarta ta kara yin gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje, da kuma kara kyautata yanayinta na kasuwanci bisa doka. (Sanusi Chen)