logo

HAUSA

Kungiyar G7 na da babban nauyi na taimakawa yaki da COVID-19

2021-06-10 16:24:58 CRI

Kungiyar G7 na da babban nauyi na taimakawa yaki da COVID-19_fororder_0610-1

Yayin da ake daf da bude taron kungiyar G7, na kasashe masu karfin ci gaban masana’antu a Birtaniya, masharhanta da dama na ganin a matsayinta, ta kungiya dake kunshe da kasashe masu wadata, tana da babban nauyi na tabbatar da ta ba da gudummawar ta, a fannin yakin da duniya ke yi da annobar COVID-19.

Sanin kowa ne cewa, yanzu haka batun samar da isassun alluran rigakafi masu inganci bisa daidaito, shi ne muhimmin mataki da masana suka amince da shi, na shawo kan wannan annoba. Kuma sassan kasa da kasa da hukumomin da batun ya shafa, ciki har da hukumar lafiya ta duniya WHO, sun sha yin kiraye kiraye, na a hada kai domin kawo karshen rashin daidaito a fannin raba rigakafin.

Ko da yake kasashe mambobin G7, da ma sauran kasashe masu wadata, sun yi namijin kokari wajen yiwa kaso mai tsoka na al’ummun su rigakafin cutar, amma hakan kadai ba zai wadatar ba, domin kuwa tuni masana suka sha bayyana cewa, muddin ba a yiwa kaso mai yawa na al’ummun duniya daban daban wannan rigakafi ba, to aikin zai zamo tamkar “Aikin Baban giwa”.

Hakan na nufin ko da kasashen G7 sun kai ga cimma nasarar shawo kan annobar a cikin gida, rashin tallafawa sauran sassa na duniya wajen kawo karshen cutar, na iya haifar da koma baya ga yakin da ake yi da ita. Idan kuma har hakan ta faru, to burin da ake da shi na sake farfadowar tattalin arzikin duniya cikin sauri zai fuskanci cikas.

Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa, kasashe masu wadata ciki har da mambobin G7, sun mallaki kaso sama da 80 bisa dari, na daukacin rigakafin da ake da shi, yayin da sauran kasashe marasa karfin tattalin arziki ke da kaso 0.3 bisa dari na rigakafin. Matakin da ke haifar da babban kalubale ga irin wadannan kasashe ta fuskar yaki da annobar.

Kari kan hakan, wasu masana na ganin wani nauyi dake wuyan G7, shi ne tabbatar da kasashe mambobin ta, sun kara rungumar akidar cudanyar sassa daban daban, da kuma goyon bayan manufar yaki da sauyin yanayi.

Ko shakka ba bu, mambobin kungiyar G7 na kunshe da kasashe mafiya samun bunkasuwa a fannin tattalin arziki, da jagoranci, da karfin fada a ji. Don haka tasirin su wajen yaki da COVID-19, da kyautatuwar tsarin kiwon lafiyar duniya na da tasirin gaske, wanda dukkanin duniya ke matukar bukata a wannan lokaci.