logo

HAUSA

Zaunannen kwamitin NPC ya kira taro kan yadda za a kyautata aikin jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa

2021-06-10 13:10:19 CRI

Zaunannen kwamitin NPC ya kira taro kan yadda za a kyautata aikin jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa_fororder_kaya

A halin da ake ciki yanzu, kasar Sin tana fuskantar matsin lamba wajen jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa, sakamakon yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, a don haka jiya Laraba zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin wato NPC ya kira taro karo na 29, domin tattauna yadda za a kyautata aikin.

Jiya zaunannen kwamitin NPC ya kira taron amsa tambayoyi kan “Aikin gina hadadden tsarin zamani na yin jigilar kayayyaki da majalisar gudanarwar kasar Sin take yi”, inda aka gabatar da tambayoyi kan wasu batutuwan da suka fi jawo hankalin mahalarta taron, wadanda suka kunshi yadda za a kyautata aikin jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa, da yadda za a gina tsarin jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa mai inganci kuma bisa dogaro da kanta.

Yayin taron da ya samu halartar shugabannin hukumar sufuri da jigilar kayayyaki, da hukumar zirga-zirgar jiragen saman fasinjoji, da hukumar kasuwancin kasar, mambar zaunannen kwamitin majalisar Tian Wei ta gabatar da cewa, “Tambayoyina su ne, na farko, yadda za a gina tsarin jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa mai inganci kuma bisa dogaro da kanta? Na biyu, yadda za a gaggauta ci gaban aikin jigilar kayayyaki ta jiragen saman dakon kaya?”

Hakika tambayoyin da madam Tian Wei ta gabatar sun fi jawo hankalin mahalartan taron, saboda aikin jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa da ake gudanarwa a halin yanzu, wato lokacin da ake fama da matsalar yaduwar annobar COVID-19, yana kara fuskantar matsin lamba, musamman ma kasa isar da kayayyaki zuwa ga masu sayayya, da kuma hauhuwar farashin jigilar kayayyaki da sauransu.

Shugaban hukumar zirga-zirgar jiragen saman fasinjoji ta kasar Sin Feng Zhenglin ya bayyana yayin da ake gabatar masa tambaya cewa, duk da cewa, adadin kayayyakin da kasar Sin take jigilar su tsakanin kasa da kasa ya kai matsayi na biyu a duniya, amma aikin jigilar kayayyaki tsakanin kasa da kasa ta jiragen sama ba shi da karfi, yana mai cewa, “Yanzu gaba daya akwai jiragen saman dakon kaya 190 a kasarmu, amma adadin ya kai kaso 25 bisa dari ne kawai idan aka kwatanta da kamfanin FedEx na Amurka, mun dade muna yin amfani da hanyar dakon kaya ta jiragen saman fasinja, a sanadin haka, mun gamu da matsala saboda layin jiragen saman kasa da kasa ya katse yayin kandagarkin annobar COVID-19.”

Feng Zhenglin ya kara da cewa, nan gaba za a taimakawa kamfanonin jigilar kayayyaki ta jiragen saman dakon kaya wadanda suke da karfin gudanar da aikin, ta yadda za su samu damar yin takara da manyan kamfanonin ketare, kana za a kara mai da hankali kan gina cibiyar sauke kayayyaki a ketare, da kyautata kayayyakin jigilar kayayyaki a filin saukar jiragen sama, da kyautata muhallin kasuwancin jigilar kayayyaki ta jiragen saman dakon kaya da sauransu. A cewarsa: “Muna fatan bayan kokarin da muke, za mu cimma burin isar da kaya cikin kasar ta jirgin saman dakon kaya cikin kwana daya kacal, da kuma isar da kaya tsakanin kasar Sin da kasashen dake makwabtaka da ita cikin kwanaki biyu, da isar da kaya zuwa manyan biranen cinikayya a fadin duniya cikin kwanaki uku. ”

An lura cewa, jigilar kaya yana shafar batun makamashi, da fidda hayaki mai tattare da sinadarin carbon, kuma alkaluma sun nuna cewa, adadin hayaki mai tattare da sinadarin carbon da sana’ar sufuri ta fitar, ya kai kaso 15 bisa dari na daukacin hayakin da aka fitar a kasar Sin, a sanadin haka akwai muhimmanci a ingiza ci gaban sana’ar ba tare da gurbata muhalli ba.

Mataimakin daraktan hukumar yin kwaskwarima da samun ci gaba ta kasar Sin Hu Zucai ya bayyana yayin da yake amsa tambayar da aka yi masa cewa, ya dace a yi hanzarin kafa tsarin sufuri wanda zai rage fitar da hayaki mai tattare da sinadarin carbon, a sa’i daya kuma, ya dace a ingiza gine-ginen sufuri na zamani, ta yadda za a cimma burin kiyaye muhalli yayin da ake raya aikin sufuri.(Jamila)