logo

HAUSA

Kasar Sin Ba Barazana Ba Ce Ga Duniya

2021-06-09 16:37:08 CRI

Kasar Sin Ba Barazana Ba Ce Ga Duniya_fororder_0609-1

Kasar Sin da mahukuntanta, sun sha nanatawa a dandali da taruka daban-daban cewa, buri da manufar kasar Sin a kullum, shi ne tabbatar da ci gaba da zaman lafiyar duniya baki daya, sabanin yadda wasu kasashe ke kallo da ma yada jita-jtar cewa, wai ci gaban kasar Sin, baraza ce ga duniya. Wannan ne ma ya sa kasar Sin ke fatan musamman Amurka da sauran kawayenta, za su rika yiwa ci gaban Sin kallo na idon basira, ta yadda za su dakatar da yada farfagandar nan maras tushe ta daukar ci gaban Sin a matsayin barazana.

Wani tsokaci da shugaba Biden na Amurka ya yi, wanda aka kuma wallafa a jaridar “The Washington Post”, a cikinsa ya kira taron kungiyar G7, a matsayin wata dama ta karfafa alakar dake tsakanin kasarsa da kawayen ta, wajen tunkarar Sin da Rasha. Abin da masu sharhi ke cewa, wannan ba shi ne hurumin da ya dace na tattauna alakar kasa da kasa ko neman bata sunan wata kasa da nufin cimma wata boyayyiyar manufa.

Sanin kowa ne cewa, hanya mafi dacewa ta warware duk wasu batutuwa da suka shafi kasa da kasa, ita ce tattaunawa da dukkanin kasashe masu ruwa da tsaki, maimakon ware kai, da mayar da wasu saniyar ware, da zage damtse wajen gudanar da komai a bayyane, da shigar da kowa, tare da ci gaba da shawarwari da hadin gwiwa, maimakon yada zarge-zarge marasa tushe.

Bugu da kari, shata layi saboda bambancin akida, da hada wata tawagar nuna wariya kan wasu kasashe, da yayata manufar ware kai tare da ’yan kanzagi, dukkaninsu sun sabawa akidun zamanin yau, kuma ba za su yi wata nasara ba. Hannu daya kuma, ba shi daukar jinka.

Ya kamata irin wadannan kasashe su san cewa, yanzu zamani ne na cude ni-in-cude ka, da martaba ka’idoji da dokoki na kasa da kasa da duniya ta amince da su, sabanin kokarin da wasu ke yi na nuna fin karfi ko dannayi ko, safawa saura bakin fenti, ko neman zama mai son kakabawa sauran kasashe ka’idojin na tilas.

Don haka, ya dace a rika martaba zabin kasashe na samun bunkasuwa, maimakon fakewa da wani batu na siyasa ko wata manufa da nufin cimma wata moriya ko neman tayar da fita a sauran kasashe ba. Kowa ne Tsuntsu kukan gidansu yake yi. (Ibrahim Yaya)