logo

HAUSA

Kasar Sin na daukar matakai don kare muhallin halittun teku

2021-06-09 14:22:05 cri

Ranar 8 ga watan Yuni na bana ita ce "Ranar Teku ta Duniya" karo na 13, kana "Ranar yada bayanan da suka shafi Teku na Kasar Sin" karo na 14. Taken ranar na bana shi ne: "Kare muhallin halittun teku, da samun daidaito tsakanin dan Adam da halittu". A cikin 'yan shekarun nan, an kiyaye wuraren da nau’o’in halittun ruwa na kasar Sin wadanda da kyar ake iya ganinsu ke rayuwa, kuma yanzu haka, wasu halittun dake cikin teku suna murmurewa sosai.

A kwalejin nazarin kimiyyar halittun ruwa na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin, wasu yayan damisan ruwa da suka rabu da iyayensu mata suna girma yadda ya kamata a karkashin kulawar ma'aikata. Ma’aikatan sun ce, bayan da wadannan yaya suka samu lafiya, za a horar da su zama a daji, don tabbatar da cewa, za su iya zama a daji lami lafiya bayan an sake su.

“Masu kiwon suna gudanar da ayyukan yau da kullun a ko wace safiya, kamar canza ruwa, tsabtace kandami, da ciyarwa. Likitan dabbobi yana lura da su a kan lokaci a ko wace rana.”

Kasar Sin na daukar matakai don kare muhallin halittun teku_fororder___172.100.100.3_temp_9500031_1_9500031_1_1_855713f2-7fb5-447b-9018-b62ab859b1ce

Domin kare wannan nau'in halittu da ke daf da karewa daga ban kasa, kasar Sin ta kafa yankunan kiyaye halittu masu yawa, muraba’in hadin ruwa na yankunan ya zarce kadada miliyan 1.56.

Baya ga kafa yankunan kiyaye halittu da aiwatar da ceto, kyankyasa bisa taimakon dan Adam, ita ma muhimmiyar hanya ce ta kare halittu masu daraja da ke daf da karewa daga ban kasa. A yankin kiyaye halittun kunkuru na Huidong dake lardin Guangdong, an taimakawa kunkuru wajen yin kwai da kyankyasa. Mai fasahar Li Manwen ya bayyana cewa,

“Koren kunkuru da aka kyankyashe bisa taimakon dan Adam a bara yana da lafiya yanzu, ko wace rana mu sauya ruwan, mu kuma wanke tafkin, sannan mu shafa masa wasu magunguna a jikinsa, saboda yadda dabbobi suka saba cizon juna, idan ba mu shafa masa magunguna ba, zai iya kamuwa da cututtuka.”

Kasar Sin na daukar matakai don kare muhallin halittun teku_fororder___172.100.100.3_temp_9500031_1_9500031_1_1_4cf32654-94fc-4b14-a12f-84f2fda0dd34

Bayanai na cewa, tun lokacin da aka kafa yankin kiyaye halittun, a jimilce an kiyaye kunkurun daji da suka haifu a bakin teku har sau 741, kuma an sake kunkuru sama da 64,000. Game da wannan, Yu Chong, babbar wakiliyar ofishin kungiyar ceton namun daji, wato wata kungiyar kare muhalli ta kasa da kasa dake Beijing, ta ce a matsayinsu na muhimman halittu, kunkuru dake rayuwa a teku suna taka muhimmiyar rawa kan dukkanin halittu masu rai na teku. A cikin 'yan shekarun nan, matakan kiyaye kunkurun teku da kasar Sin ta dauka na inganta.

“A cikin shekarun da suka gabata, a bisa kokarin wasu hukumomin kare kunkurun teku da kuma goyon baya daga wajen gwamnati, kasar Sin ta gudanar da wasu ayyukan gwaji na hada gwiwa tsakanin al’ummomi don kare kunkuru dake rayuwa a teku, kuma ta hanyar hadin kan al’ummomi da ba da horo a fannin ceto, an wayar da kan masunta game da kare muhalli. Wani batu kuma da ya zama dole a ambata shi ne, a cikin sabon jerin sunayen muhimman namun daji dake bukatar a kiyaye su da aka gyara a wannan shekarar da muke ciki, an daga matsayin nau'ikan kunkurun teku guda biyar da ke zama a kasarmu daga matsayi na biyu zuwa na farko. A ganinmu, wannan mataki ne mai matukar muhimmanci .”

Kyakkyawan yanayin muhallin halittu na teku, shi ne tushen samun wadatattun halittu a ruwa.

A ganin Yu Chong, wannan daidai ne saboda sanin tasirin da sharar leda ke kawo wa teku da kuma muhallin halittu, a ‘yan shekarun nan, kasar Sin na kara kokarinta wajen rage samarwa da amfani da kayayyakin roba da ba su wajaba ba. Ta ce,

“Bisa manufofin da gwamnati ke dauka, a zahiri ana ina ganin yadda aka fito da alamu mai tabbaci kuma mai karfi na rage yiwuwar gurbata muhalli sakamakon kayayyakin roba da ba za a iya sake amfani da su ba, wannan ya nuna ra’ayin kasar Sin na rage sharar roba, kuma hakan zai taimakawa jama'a wajen shiga a dama da su kan batutuwan da suka shafi rage kayayyakin roba da ayyukan kare muhalli. Wannan wata babbar nasara ce da aka samu.” (Bilkisu Xin)