logo

HAUSA

Kasashen Yamma Sun Sake Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Xinjiang

2021-06-09 16:58:25 CRI

Kasashen Yamma Sun Sake Nuna Fuska Biyu A Kan Batun Xinjiang_fororder_007Xa9vuly4gr9x0x42gij30o00dhake

Daga Amina Xu

Kwanan nan, jaridar “The Guardian”ta Nijeriya ta ba da labari cewa, wani rukuni a birnin London dake binciken mawuyacin halin da ‘yan kabilar Uygur ke ciki a kasar Sin ya saurari bayanai daga shaidu, kan zargin wai an ci musu zarafi, sai dai gwamnatin Sin ta nuna matukar rashin jin dadin kan wannan batu da ta ce karya ce.

Hasali ma dai an sha samun irin wadannan labarai a baya-bayan, inda kasashen yamma ke yunkurin takalar yanayin kare hakkin bil-Adama na kasar Sin, musamman ta hanyar kirkirar labarin karya kan jihar Xinjiang da sauran sassan kasar, da nufin shafawa Sin bakin fenti. Har ma a baya-bayan nan, an kafa kotun musamman kan Uygur a London don sauraran kalaman wasu da suka ce wai an ci musu zarafi a jihar. Shin ko da gaske ne ‘yan kabilar Uygur suna rayuwa cikin mawuyacin hali? Bari mu gabatar muku wani labari dangane da wasu ‘yan uwa biyu ‘yan kabilar Uygur.

Guli babba da Guli karama ‘yan kabilar Uygur ne, kuma su kan bayyana yadda suke gudanar da rayuwarsu na yau da kullum a shafukan Intanet.  A shafinsu mai suna “Yadda Guli ke kallon Xinjiang” da suka bude a kan Twitter, ana iya ganin yanayin jihar Xinjiang cikin mintoci kadan ta bidiyon da suka wallafa, ta wannan hanya, Guli suna fatan ‘yan kasashen waje su fahimci hakikanin Xinjiang da karairayin da kasashen yamma suke yadawa na cewa wai ana tilasta mutane su yi aiki ko keta hakkin Bil Adama a wurin. A bidiyon da suka wallafa, Guli sun ce, jama’a na rayuwa cikin kwanciyar hankali da walwala a wurin, zaman rayuwarsu babu bambanci da na sauran wuraren kasar, a shekarar bara duk da yaduwar cutar COVID-19, masu yawon shakatawa da yawansu ya kai miliyan 150 sun ziyarci yankin. Amma, Twitter ya rufe shafinsu bisa dalilai biyu, wato shafin ya sarrafa ra’ayin jama’a don ganin yana da mabiya da yawa da wasu shahararrun mutane sun nuna sha’awa ga abin da ake wallafawa a shafin, da kuma wallafa wasu labarai marasa kyau. Bari mu kuma bibiyi abin da Guli suka wallafa a shafin. A wani bidiyon da Guli suka wallafa, sun amsa wasu sakwannin da aka turo musu da cewa, ba sa jin dadin matakan da wasu kasashen yamma suka dauka.  Sun ce, wasu na nuna bambancin ra’ayi kan jihar saboda ba su fahimci wannan jiha ba sosai. Amma yanzu suna ganin cewa, wasu suna yin kunnen uwar shegu game da hakikanin Xinjiang.

A ganina, an rufe shafin Guli ne saboda sun dakushe makarkashiyarsu na ‘yancin fadi albarkaci da kare hakkin Bil Adama. Bidiyon da Guli suka wallafa ba ma kawai sun karyata karairayin da kasashen yamma suka yi kan Xinjiang game da batun kare hakkin Bil Adama ba, hatta ma ya dakile yunkurin da suka yi na zama “abin koyi a fannin kare hakkin Bil Adama” a duniya. Suna jin tsoro sosai game da gaskiya da hakikanin halin da ake bayyana a kan Intanet, saboda hakan ba za su iya sauya tunanin jama’arsu game da takalar kasar Sin. Saboda haka, sun rufe shafin Guli.

Kasashen yamma sun furta kalaman kare hakkin Bil Adama da ‘yancin mutum bisa ma’auninsu kawai. Yadda suke neman bata sunan kasar Sin kan jihar Xinjiang, ba shi da alaka da rashin fahimtar jihar, suna yin haka ne kawai, don hana bunkasuwar kasar Sin da kawo mata baraka. (Amina Xu)