logo

HAUSA

Yawan sabbin masu harbuwa da cutar Covid-19 a fadin duniya ya ragu cikin makwanni 6 a jere

2021-06-08 14:15:03 CRI

Yawan sabbin masu harbuwa da cutar Covid-19 a fadin duniya ya ragu cikin makwanni 6 a jere_fororder_微信图片_20210608141431

Alkaluman kididdigar da hukumar lafiya ta duniya(WHO) ta fitar na nuna cewa, yawan sabbin masu harbuwa da cutar Covid-19 a fadin duniya ya ragu cikin makwanni shida a jere, sai dai hukumar ta yi gargadin cewa, yadda cutar ke sauye-sauye akai-akai, ya sa ta kara karfin bazuwa, don haka, ya zama dole kasa da kasa su rika yin taka tsantsan, kuma yawaita yiwa mutane rigakafi, ita ce hanyar magance wannan batu. Lubabatu na dauke da karin haske.

A yayin taron manema labarai da aka gudanar a jiya Litinin, babban darektan hukumar WHO Dr.Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, ga alama, an fara samun sassaucin yaduwar annobar Covid-19, kuma abu ne dake ba mutane kwarin gwiwa. Ya ce,“Yawan sabbin masu harbuwa da cutar Covid-19 da aka ba da rahotonsu ga WHO ya ragu cikin makwanni shida a jere, a yayin da yawan mamata a sanadiyyar cutar ma ya ragu cikin makwanni biyar a jere. Duk da haka, yanayin da ake ciki a sassan duniya daban daban ya bambanta. A makon da ya gabata, akwai wasu shiyyoyi uku da aka samu karuwar mamatan, wadanda suka hada da Afirka da nahiyar Amurka da kuma yankin yammacin tekun Fasifik. Don haka, abin da muke gani shi ne, har yanzu kasashe da yawa suna fuskantar hali mai hadari sosai, a yayin da wasu kasashen da suka yi wa al’ummarsu da dama rigakafi, sun fara tattauna matakan kawo karshen kandagarki da suka sanya.”

Mista Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce, dole ne kasashen da suka samu sassaucin yaduwar cutar su yi taka tsantsan wajen sassauta matakan kandagarki. Sabo da bisa ga yadda cutar ke rika sauyawa, musamman ma nau’in cutar da ta sauya kama a kasar Indiya da ake kira Delta da sauransu suke kara yaduwa a duniya, lalle janye matakan kandagarki cikin sauri zai iya zama masifa ga al’ummomin da ba su samu rigakafi ba.

Dr.Maria Van Kerkhove, jami’ar WHO mai kula da fasahohi ta yi nuni da cewa, ya zama dole a yi taka tsantsan game da yadda cutar ke sauyawa. Ta ce,“Hakika nau’in Delta ya fi Alpha saurin bazuwa, wadda yanzu haka take yaduwa a kasar Burtaniya, tare da sauran kasashe sama da 60. A yayin da cutar Covid-19 ke ci gaba da yaduwa, za a ga yadda cutar ke kara sauyawa, kuma abin da ke damun mu shi ne yadda cutar take sauyawa ta kara karfin bazuwarta, baya ga kuma yadda al’ummomi ke kara cudanya da juna, da yadda aka sassauta matakan kandagarki, da ma rashin daidaiton raba rigakafi, duk suna kawo mana hadari sosai.”

A yayin taron manema labarai da aka shirya a wannan rana, Dr.Michael Ryan, darektan zartaswar shirin gaggawa na WHO ya yi nuni da cewa, kasashen da suka dauki matakan da suka dace game da kandagarkin cutar, yanzu suna fuskantar wahalar sake bude kofarsu. A sakamakon nasarorin da suka samu wajen kandagarkin cutar, shi ya sa suke fuskantar karin hadari fiye da sauran kasashe, kuma mafita wajen daidaita matsalar ita ce su yi wa sama da kaso 80% na al’ummominsu rigakafi, kuma hakan zai iya sassauta hadarin da za a fuskanta ta bangaren masu kamuwa cutar da za su iya shiga kasashen. Ya ce,“Sabo da haka, sake bude kofarsu zai iya zama kuduri mai wahala ga kasashe da yawa wadanda suka dade da samun ‘yan kalilan dake harbuwa ko ma babu. Cutar za ta iya sake shiga kasashen idan sun sake bude kofarsu, daga wasu kasashen da ba su kai ga shawo kanta ba. A cikin irin wannan hali, dole ne kasashen su kiyaye tsarin ko ta kwana, haka kuma ya zama dole su kara yi wa al’ummominsu rigakafi. Wato ke nan, kara yi wa al’umma rigakafi, ita ce mafita ga kasashen idan har suna son fita daga yanayin annobar.”