logo

HAUSA

In ana tuya bai kamata a manta da albasa ba

2021-06-08 16:19:19 CRI

In ana tuya bai kamata a manta da albasa ba_fororder_0608-1

Majalisar Dinkin Duniya ta bude wani taron manyan jami’ai da ya fara gudana tun daga jiya Litinin zuwa Alhamis 10 ga wata, domin nazarin alkawarin da duniya ta yi na kawo karshen cututtukan Kanjamau da na Tarin Fuka zuwa karshen shekarar 2030 da kara jaddada kudurin. Bisa gayyatar da aka yi mata, uwargidan shugaban kasar Sin, Peng Liyuan, ta gabatar da jawabi ta kafar bidiyo a jiyan. Peng Liyuan ta kasance jakadiyar hukumar Lafiya ta duniya kan yaki da cututtukan biyu, kuma ta taka rawa gaya tare da bayar da gudunmawa ga kokarin gwamnatin kasar Sin na yaki da cututtukan. Haka kuma ta hada hannu da matan shugabannin kasashen nahiyar Afrika domin yaki da wadannan annoba.

Kanjamau da Tarin Fuka, cuttuttuka ne da har yanzu kasashen duniya ke kokarin ganin bayansu saboda yadda suke da saurin yaduwa da kuma sanadin mutuwar mutane masu tarin yawa. Kiran wannan taro a irin wannan lokaci da duniya ta mayar da hankali kan yaki da annobar COVID-19, abu ne da ya yi matukar da cewa, domin bai kamata a rika tuya ana mantawa da albasa ba.

A cewar Madam Peng Liyuan, yakin da duniya ke yi da cututtukan Tarin Fuka da Kanjamau, ya samu dimbin sakamako a shekarun baya-bayan nan, saboda hadin kan da al’ummun duniya suka bayar. Lallai ana matukar bukatar wannan hadin kai ya ci gaba a yadda yake, kome ya kara karfi domin ganin an kawo karshen cuttutukan baki daya. Babu wani sakamako da za a samu dangane da abun da ya shafi dukkanin bil adama, ba tare da hadin kai tsakanin al’ummomi da ma gwamnatoci ba.

Ta ce sannu a hankali, kasar Sin ta kafa wata dabara ta hadin gwiwa tsakanin cibiyoyin kandagarki da dakile cutar Kanjamau da takwarorinsu na cutar Tarin Fuka, lamarin da ya kai kasar ga rage matakin yaduwar cututtuka cikin shekaru 20 da suka gabata, inda yaduwar Tarin Fuka ya ragu da kaso 40, adadin mace-mace sanadiyyarsa kuma ya ragu da sama da kaso 70, tana mai alakanta nasarorin da kokarin gwamnatin kasar da na jami’an lafiya da masu bayar da gudunmawa. Yayin da ake hadin gwiwa da hada hannu tsakanin al’ummomin da gwamnatoci, ya kamata kuma a yi koyi da wasu dabarun da suka haifar da nasara. Wato irin wannan dabara ta kasar Sin, ta cancanci a yi koyi da ita domin irin tasirin da ta yi. Ya zama wajibi a rika gwaji da sauya dabaru domin samun mafi dacewa wajen ganin a yaki cututtukan. Haka zalika, ya kamata a fahimci cewa, gwamnati ita kadai ba za ta iya aikin ba, tana bukatar goyon bayan jami’an lafiya da ma jama’arta, domin a gudu tare a tsira tare.

Cututtuka masu yaduwa sun kasance kalubalen bai daya dake fuskantar dan adam, haka zalika burinsu ne kawar da wadannan cututtuka. Barkewar annobar COVID-19 ta haifar da karin kalubale ga kokarin dakile cututtuka, duk da cewa yaduwarsu ba ta yi karfin ta COVID-19 ba, akwai bukatar a kara hada hannu da zage damtse kamar yadda aka yi wajen yaki da COVID-19 domin kare rayuka da samar da al’umma mai kyakkyawar makoma ga daukacin bil adama. (Fa’iza Mustapha)