logo

HAUSA

Abdullahi Mustapha: Na karu sosai a kasar Sin

2021-06-08 14:46:54 CRI

Abdullahi Mustapha: Na karu sosai a kasar Sin_fororder_微信图片_20210608124451

Abdullahi Mustapha, wanda aka fi sani da suna malam Bako a makaranta, dalibin Najeriya ne wanda ke dab da kammala karatunsa na neman digiri na farko a jami’ar nazarin fasaha ta Shenyang university of Chemical Technology dake birnin Shenyang na lardin Liaoning a arewa maso gabashin kasar Sin.

A zantarwarsa da Murtala Zhang, malam Bako ya bayyana takaitaccen tarihinsa, da babban dalilin da ya ba shi sha’awar zuwa karatu a kasar Sin. Malam Bako ya kuma bayyana fahimtar sa game da bambancin yanayin karatun dake kasancewa tsakanin Najeriya da kasar Sin, da kuma yadda al’adun gargajiyar kasar suka burge shi, musamman wani biki mai suna Duanwu, da al’adar cin Zongzi a bikin.

A karshe, Malam Bako wanda zai ci gaba da karatunsa na neman digiri na biyu a kasar Sin, ya yi kira ga matasan Najeriya su tashi tsaye don neman karo ilimi, da kokarin neman na kansu.(Murtala Zhang)