logo

HAUSA

Xun Xiaohong: Zan yi ko wane aikin da zai amfani al’ummar Sin

2021-06-07 10:56:46 CRI

Xun Xiaohong: Zan yi ko wane aikin da zai amfani al’ummar Sin_fororder_1

Xun Xiaohong, shugabar tawagar Xun Xaihong ta kamfanin kula da magudanan ruwa na Harbin (HDG) dake lardin Heilongjiang na arewa maso gabashin kasar Sin, na alfahari da kasancewarta wata mambar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin. Dukkan iyayenta sun kasance mambobin jam’iyyar. Da taimakonsu, Xun ta zama ma’aikaciyar tsafta. Ta samu damarmakin karin girma a fannin aikinta, amma sai ta zabi ta zauna a inda take. A lokacin da ta kai shekarar ritaya a watan Yulin 2020, Xun ta zabi ta ci gaba da aiki. A duk lokacin da aka samu mahaukaciyar guguwa, ko wuri ya yi kankara saboda sanyi, Xun da tawagarta na sauke nauyin dake wuyansu na tsaftace magudanan ruwa ba dare ba rana a Harbin. Kokarinsu ya bada gudunmuwa ga tabbatar da kyakkyawan muhali da tsaftar birnin. 

Har yaushe mutum zai ci gaba da zama a wurin dake cike da kazanta da wari da bola? Xun Xiaohong ta saba da irin wannan wuri. Ta shafe tsawon shekaru 30 tana aikin tsaftace magudanar ruwa. “zan yi duk wani aiki da zai yi kyau ga Jam’iyya da al’umma. Zan dauki aikin a matsayin sana’ata, haka kuma burin da nake son cimmawa”, cewar Xun.

Xun ta girma a gidan kakanninta. Dukkan kakanninta tsoffin sojoji ne masu biyayya ga Jam’iyya. Harrufan Sinanci na farko da Xun ta koya ba sunanta ba ne, sun kasance taken “hidimtawa jama’a da zuciya daya”. Tun Xun tana ‘yar karama aka koya mata yadda za ta zama mai amfanawa kasa da al’ummarta. “Ina alfahari da cewa galibin dangina mambobin Jam’iyya ne. na yi ammana cewa, ni ‘ya ce ga Jam’iyyar,” cewar Xun.

A shekarar 1991, Xun ta yanke shawarar zama ma’aikaciyar tsafta. Mamanta ta tambaye ta ko za ta iya aikin na tsafta mai wahala duk rintsi. Xun ta amsa da cewa “idan wasu za su iya, ni ma zan iya!”

Mahaifiyar Xun ma ma’aikaciyar tsafta ce, a lokacin da take karama, kuma ta samu lambobin yaba a mabanbanta lokuta a matsayin abar koyi. Ta shaidawa Xun cewa, “aikin mai bukatar gaggawa ba shi da isassun ma’aikata. Idan kika jajirce, za ki yi aiki mai kyau. Ki yi abubuwan da za su amfanawa kasa da al’ummarta.”

Yayin da kalmomin mahaifiyarta suka darsu a zuciyarta, Xun ta rike aikinta da kyau. A watan Yunin 2004, ta shiga Jam’iyya. Ta karbi rantsuwar shiga Jam’iyyar, kuma ta yi alkawarin zama cikin shiri a ko da yaushe, domin ta sadaukar da komai ga Jam’iyya da al’umma.

“ A shekarar 2005, kamfaninmu ya kafa wata tawagar ma’aikatan tsafta ta mata, wadda ta kunshi ma’aikata 5 da kuma ni. Yanzu tawagar na da karin mambobi. Aikinmu ya hada da tsaftacewa da kula da magudanan ruwa, gyara kayayyaki da janye ambaliya,” cewar Xun. Aikin ya zama wani bangare na rayuwarta. Ta sadaukar da kanta ga aikin da kuma birnin.

“A Harbin, yanayi mafi sanyi ka iya kai wa maki 32 kasa da 0,” cewar Xun. A lokacin da ita da abokan aikinta suka sanya rigunan aiki a lokacin hunturu, wandunansu kan yi karfi sosai. Sai sun sanya safar hannunsu a cikin aljihu, kuma dole ne su sanya safar hannu kafin su shiga cikin magudanan.

Xun Xiaohong: Zan yi ko wane aikin da zai amfani al’ummar Sin_fororder_2

A lokacin zafi kuma, dole ne su jure iska mai dumi na cikin magudanan. A kowacce rana a lokacin zafi, suna bukatar tsaftace matsakaicin adadin magudanan ruwa 140 tare da tsaftace kimanin cubic mita 6 na tabo a lokacin hunturu. Suna kuma tunkarar iftila’i kamar ambaliya. 

Bisa la’akari da kasancewar Harbin a gabar kogin Songhuajian, tawagar Xun na fuskantar kalubale mai tsanani a kowanne lokacin ambaliya. A lokacin zafi, ma’aikatan kan yi bacci tagarsu a bude. Idan suka ji an fara ruwan sama, nan take suke tashi su duba yanayin ruwan. Idan yana da karfi, su kan fita su je aikin janye ruwa daga yankuna masu ambaliya.

A ranar 12 ga watan Agustan 2016, ruwan sama kamar da bakin kwarya sanaddiyyar guguwa, ya haifar da ambaliya mai tsanani a fadin sassan Harbin. Domin tabbatar da tsaron rayukan mutane har ma da na ababen hawa, Xun da tawagarta sun yi aikin tsawon sa’o’i 13 cikin ruwan da ya kai tsawon gwiwoyinsu har sai da ambaliyar ta sassauta.

A ranar 12 ga watan Yunin 2016 kuma, aka fuskanci ruwa mai karfi da kankara a Harbin. Cikin gaggawa tawagar Xun ta isa wurin. Kankarar ta sanya ganyayyaki zubowa daga bishiyoyi, inda suka toshe magudanan ruwa. Sai da mutanen dake zaune a yankin suka nemi mafaka a wurare masu tudu.

Xun ta zama ta farko ta shiga cikin ruwan mai sanyi domin bude murafen magudanan ruwa. Abokan aikinta na biye da ita. A ranar, ma’aikata 500 na kamfanin kula da magudanan ruwa na Harbin ne suka yi aikin shawo kan ambaliya a sassa daban daban na Harbin har zuwa tsakar dare.

Tsaye a kan titi, da murfin magudana a tsakanin kafafunta, Xun da kanta ta zama alamar hanya ga motocin dake wucewa.

Wani mai wucewa ya dauke ta hoto a hakan, sannan ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Hoton ya yi ta yawo a kafar sada zumunta, inda ya sa Xun zama tauraruwa a kafar intanet.

An samu barkewar COVID-19 a kasar Sin ne kafin bikin Bazara na shekarar 2020. A ranar 11 ga watan farko na kalandar gargajiya ta kasar Sin, wata magudanar ruwa ta wata unguwa a Harbin ta toshe. Ruwa mai dauda ya taro, wanda ya hana mazauna shige da fice.

Bisa la’akari da tabbatar da wasu a unguwar sun kamu da cutar, ba za a iya tantance ko ruwan na dauke da kwayoyin cutar ba ko a’a. Xun ta sanar da shugabanninta, inda aka tura ta da tawagarta domin gyara magudanar ruwan.

Xun da abokan aikinta sun sanya marufin baki da hanci inda suka yi amfani da na’ura wajen bude hanyar ruwa tare da tsaftace bututan ruwan gidajen unguwar.

A lokacin da annobar ta yi tsanani a Harbin, tawagar Xun ta nemi tsaftace magudanan ruwa dake yankunan da aka kebe don ma’aikatan jinya, bisa radin kansu. Wannan ya tabbatar da tsabtar wurin. 

Duk da cewa ma’aikaci na aiki ne a fili, dole ne ya zama mai basira. Wani lokacin a kan binne ko rufe manya magudanan ruwa ba bisa ka’ida ba a cikin birane, wanda ke ba ma’aikata wahalar ganowa. Idan magudanan ruwa ta toshe ko ta lalace, to ana bukatar kwarewa da gogewar ma’aikata wajen ganowa da gyara ta.

A wani lokaci, abokan aikinta sun kasa gano inda ya toshe. Sun so tona wata hanya a wurin, amma Xun ta dakatar da su. Ta dudduba wurin, sai ta gano marufin bututun. Bayan ta daga shi, abokan aikinta suka gano cewa wani karfe ne ya tsohe shi. Sai da dukkan ma’aikatan suka tafawa Xun.

Yayin ambaliyar 2015, an yi ruwa sosai, har wata magudanan ruwa ta toshe. Abokan aikin Xun sun gwada dabaru da dama amma suka gaza gano hanyar bututun. Da isowar Xun, ta saita na’urar dake bude hanyar ruwa a wurin da take tunanin hanyar take. Sai ta nemi abokan aikinta su rika kara karfin na’urar a hankali. A karshe sun bude bututun da ya toshe.

“Ya kamata a ce ma’aikaci ya goge kan aikinsa, sannan ya ci gaba da tunanin hanyoyin inganta basirarsa. Dabaru masu kyau za su taimakawa kwarewarmu, da rage wahalar aiki,” cewar Xun.

A lokacin da aka fi hada-hada, Xun da abokan aikinta kan gyara magudanan ruwa kimanin 70 a wata guda. 

Xun Xiaohong: Zan yi ko wane aikin da zai amfani al’ummar Sin_fororder_3

A shekarun baya-bayan nan, kamfanin kula da magudanan ruwa ya kirkiro kayayyakin aiki masu amfani da dama, domin saukaka ayyukan ma’aikatansa. Domin karfafa masu gwiwar kirkire-kirkire, kamfanin na gudanar da gasa a kowacce shekara. Tawagar Xun ta jera shekaru 5 tana lashe kyautar matsayi na farko.

A watan Satumban 2017, kamfanin ya kafa wata tawaga, da aka yi wa lakabi da sunan Xun. A watan Yulin 2020 kuma, Xun ta kai shekarun ritaya. Bisa taimakon shugabannin kamfanin, Xun ta ci gaba da aiki a matsayin shugabar tawagar masu aikin sa kai. Dukkan masu aikin sa kan, mambobin jam’iyya ne. Tana kuma taimakawa wajen horar da sabbin ma’aikatan kamfanin.

Xun ta karbi lambobin yabo da dama saboda hazakarta. Lambobin sun hada da na mamban jam’iyya mai hazaka da ma’aikaciya abar koyi da lambar karramawa ta kungiyar mata ta kasar Sin. Kana an zabe ta a matsayin wakiliya yayin babban taron JKS na kasa karo na 19 a shekarar 2017.

A ranar 1 ga watan Oktoban 2019, Xun ta halarci katafaren bikin cika shekaru 70 da kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin a birnin Beijing. Tana alfahari da gayyatarta da aka yi.(Kande Gao)