logo

HAUSA

Ci gaba da baza “kwayar cutar siyasa” da wasu ‘yan Amurka ke yi ya lahanta duk duniya

2021-06-04 20:42:00 CRI

Ci gaba da baza “kwayar cutar siyasa” da wasu ‘yan Amurka ke yi ya lahanta duk duniya_fororder_A

Duk da cewa, kasar Amurka ta kasance a kurar baya a fannin dakile yaduwar cutar COVID-19 a duniya, amma har yanzu akwai wasu ‘yan kasar, wadanda ba su koyi darasi ba, inda suke neman sake shafawa kasar Sin bakin fenti bisa hujjar binciken asalin kwayar cutar, da ci gaba da baza “kwayar cutar siyasa” a fadin duniya, al’amarin da ya sake nuna babakeren da Amurka ta yi a duniya.

Kila wasu ‘yan Amurka sun manta, duba da yadda tsohuwar gwamnatin Amurka ya yi yunkurin yada shaci-fadi game da asalin kwayar cutar, yanayin dakile cutar a kasar ya tabarbare ainun. Yanzu, yawan mutanen da suka rasa rayukansu a Amurka sakamakon cutar ya wuce dubu 600.

Har wa yau, yunkurin bata sunan kasar Sin da wasu ‘yan Amurka suka yi ya kawo babbar illa ga hadin-gwiwar kasa da kasa a fannin kandagarkin cutar.

Ci gaba da baza “kwayar cutar siyasa” da wasu ‘yan Amurka ke yi ya lahanta duk duniya_fororder_B

Amurka ta yi biris da bukatun kasashe masu tasowa, amma tana ci gaba da shafawa kasar Sin bakin fenti, wadda ta nuna kwazo wajen samar da tallafi ga sauran kasashe.

Bugu da kari, game da binciken gano asalin kwayar cutar, Amurka ta sake alakanta kwayar cutar da kasar Sin, gami da rura wutar rikicin kabilanci. Kwanan nan ne aka kara samun al’amuran nunawa ‘yan asalin Asiya wariyar launin fata a kasashen Amurka da Birtaniya da kuma Australiya.

Amurka tana jin tsoron bude kofarta ga hukumar WHO don a yi mata bincike, amma ta ce wai kasar Sin ta kawo tsaiko ga aikin bincike wadda ta riga ta gayyaci kwararrun WHO don su gudanar da bincike kan asalin kwayar cutar a kasar. Kuma Amurka ta sake shafawa kasar Sin bakin fenti ba tare da wata shaida ba. Hakan ya nunawa duniya cewa, abun da wasu ‘yan siyasar Amurka suka fada game da kasancewar sassa da dama a duniya, ba haka ba ne, kana ko kadan ma Amurka ba ta sauya salon nuna babakere ba, abun da yake haifar da sabon kalubale ga tsare-tsare gami da ka’idojin kasa da kasa a halin yanzu. (Murtala Zhang)