logo

HAUSA

Ba zai yiwu a cimma nasarar hana ci gaban Sin bisa fakewa da batun Xinjiang ba

2021-06-04 13:39:34 CRI

Ba zai yiwu a cimma nasarar hana ci gaban Sin bisa fakewa da batun Xinjiang ba_fororder_xinjiang

A cikin ‘yan watannin da suka gabata, wasu rukunoni masu adawa da kasar Sin, suna ta shafawa jihar Xinjiang ta kasar Sin bakin fenti, bisa fakewa da tilastawa al’ummun jihar yin aikin dole. Game da hakan, jihar ta Xinjiang ta kira taron watsa labarai a nan birnin Beijing a jiya Alhamis.

Jihar Xinjiang ta kasar Sin ta kira wannan taro na watsa labarai ne kan batutuwan dake shafar jihar, inda aka gayyaci wasu jagororin hukumomin da abun ya shafa na jihar, da wakilan masu jagorancin sana’o’i daban daban na jihar, da masanan da abin ya shafa, da ma’aikatan dake aiki a wasu kamfanoni, domin su yi cikakken bayani kan hakikanin yanayin da jihar Xinjiang ke ciki, ta yadda hakan zai karyata jita-jitar da wasu rukunoni masu adawa da kasar Sin suke bazawa.

Mataimakin kwalejin koyar da ilmin doka ta jami’ar Xinjiang Aierken Shamushake, ya bayyana cewa, tsarin ba da tabbacin samar da guraben aikin yi na jihar Xinjiang, da matakin da ta dauka domin aiwatar da tsarin, sun dace da dokokin kasar Sin, kuma sun dace da ma’aunin hayar ‘yan kwadagon kasa da kasa, da ma’aunin kare hakkin dan Adam, haka kuma sun dace da babban burin mahukuntan kasar Sin na samar da wadata ga al’ummun kabilu daban daban dake rayuwa a jihar Xinjiang. Kaza lika daukacin kasashen duniya suna iya tantance yanayin da suke ciki ta hanyoyi daban daban.

Mataimakin shugaban kungiyar sana’ar sarrafa kayan sawa ta jihar Liu Qingjiang, ya yi tsokaci da cewa, yayin da ake gudanar da aikin sarrafa kayan sawa, yawancin kamfanonin dake jihar suna amfani da na’urorin zamani wadanda suka kai sahun gaba a duniya, wadanda kuma suka kai matsayin koli a cikin kasar ta Sin. Don haka babu yiwuwae a tilastawa al’ummun jihar yin aikin dole.

Wasu kamfanonin ketare dake kasar Sin su ma sun fitar da sanarwa, bayan da suka yi rangadin aiki a jihar Xinjiang. Alal misali, kamfanin samar da kayayyakin gida na amfanin yau da kullum na kasar Japan MUJI, ya sanar da cewa, bayan binciken da aka yi, ba a tarar da matakan da suka sabawa dokoki ba, kuma kamfanin zai ci gaba da yin amfani da audugar Xinjiang.

Shi ma kamfanin samar da kayayyakin motsa jiki na kasar Amurka Skechers, ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, bai tarar da batun tilastawa al’ummun Xinjiang yin aikin dole ba, bayan da ya gudanar da bincike kan kamfanonin kasar Sin, wadanda ke samar masa kayayyaki.

Babban sakataren rukunin masu sana’ar narka karafa ta jihar Pan Cunxiang, shi ma ya ce a cikin ‘yan makwannin da suka gabata, wasu kafofin watsa labarai sun ziyarci wasu kamfanonin narka karafa dake jihar, kuma ba su tarar da alamomin yin aikin dole ba, duba da cewa, ana yin amfani da na’urorin zamani yayin gudanar da ayyuka.

Yayin taron watsa labaran da aka kira jiya, Aikebaier Tuluhong dake aiki a kamfanin sarrafa kayan sawa na Huafu dake jihar Xinjiang, ya yi bayani kan tarihin aikinsa, inda ya bayyana cewa, “A baya na taba kiwon tumaki a kan dutse tare da babana, babu kudin shiga, inda iyali na ke fama da kangin talauci, amma yanzu ina aiki a kamfanin sarrafa kayan sawa. Abun farin ciki shi ne, na hadu da matata a kamfanin. Ko wanen wata, ni da matata muna samun kudin shiga sama da kudin Sin yuan 8000, muna jin dadin rayuwa matuka, muna son ci gaba da yin aiki a kamfanin. Nan gaba kuma, muna fatan za mu sayi dakin kwana kusa da kamfaninmu, ta yadda za mu samar da damar karatu da rayuwa mai inganci ga yaranmu.”

Sai dai kuma wasu rukunonin adawa da kasar Sin sun sanya takunkumi kan kamfanin da yake aiki, lamarin da ya yi matukar fusata shi. Ya ce, matakin da aka dauka ya shafawa garinsa bakin fenti, haka kuma ya lalata hakkokinsu.

Kakakin watsa labarai na gwamnatin jihar Xinjiang Xu Guixiang ya bayyana cewa, ko shakka babu, al’ummun kabilu daban daban na jihar suna jin dadin aiki ne a karkashin hasken rana, kuma suna yin kokari domin kyautata rayuwarsu, amma wasu kasashen yammaci suna baza jita-jitar aikin dole bisa fakewa da hakkin dan Adam, domin dakile hakkinsu na yin aiki bisa doka.

A bayyane an lura cewa, suna fatan al’ummun Xinjiang su ci gaba da rayuwa cikin duhu da talauci, da kuma koma baya. Suna son hana ci gaban kasar Sin, ta hanyar lalata kwanciyar hankalin Xinjiang, amma ko alama ba za su iya cimma wannan buri na su ba. (Jamila)