logo

HAUSA

Yadda Sin ta cika alkawarinta na samar wa kasa da kasa alluran rigakafi

2021-06-03 14:29:39 CRI

Yadda Sin ta cika alkawarinta na samar wa kasa da kasa alluran rigakafi_fororder_hoto

A ranar 1 ga watan nan, hukumar lafiya ta duniya (WHO), ta amince da amfanin allurar rigakafin COVID-19 da kamfanin hada magunguna na kasar Sin Sinovac ya samar domin amfanin gaggawa, kuma, wannan shi ne karo na biyu da allurar rigakafin COVID-19 kirar Sin ta samu amincewar WHO domin amfanin gaggawa.

Kafin wannan, a ranar 7 ga watan Mayu, WHO ta amince da amfani da allurar rigakafin COVID-19 da kamfanin Sinopharm na kasar Sin ya samar domin amfanin gaggawa, wadda ta kasance allurar rigakafi ta farko, wadda ba kirar kasashen yammaci ba, cikin wadanda WHOn ta amince a yi amfani da su na gaggawa. Lamarin da ya nuna cewa, a karo na farko, allurar rigakafin cutar mai yaduwa da kasar Sin ta samar, ta samu amincewar WHO domin amfanin gaggawa.

Dangane da wannan batu, ga karin bayani daga Maryam Yang…

Hukumar WHO ta amince da amfanin gaggawa na alluran rigakafin COVID-19 iri biyu da kasar Sin ta samar. Domin tabbatar da kyawun rigakafin, da ingancinsu, matakan da ya samar da karin gudummawa a fannin cimma nasarar yaki da annobar tsakanin kasa da kasa, musamman ma ga kasashe marasa ci gaba, wadanda suke fama da matsalar karancin alluran rigakafi.

Kwararre a fannin kiwon lafiya na kasar Sin Zhong Nanshan ya ce, yi wa galibin al’ummomi alluran rigakafi, domin kafa tsarin kariyar jama’a daga cutar COVID-19, shi ne abu mafi muhimmanci wajen dakile yaduwar cutar COVID-19. Amma, abin bakin ciki shi ne, a halin yanzu, ba a raba alluran rigakafi cikin adalci ba a sassan kasashen duniya.

Ba kamar yadda wasu kasashe masu ci gaba suka adana alluran rigakafin fiye da yadda suke bukata ba, ko kuma hana fitar da sinadaran ta zuwa kasashen ketare, kasar Sin ta yi alkawarin samar wa kasa da kasa alluran rigakafin COVID-19, a lokacin babban taron kiwon lafiya na duniya karo na 73, wanda aka yi a watan Mayu na shekarar 2020, domin bayar da gudummawar ta a fannin ba da tallafin alluran rigakafi ga kasashe masu tasowa.

Kawo yanzu, bayan shekara daya da yin wannan alkawari, kasar Sin ta riga ta samar da alluran rigakafin COVID-19 sama da miliyan 350 ga gamayyar kasa da kasa, ciki har da samar da tallafin alluran rigakafi ga kasashe sama da 80, da fitar da alluran rigakafin zuwa kasashe sama da 40, tare da yin hadin gwiwa da wasu kasashe masu tasowa domin sarrafa alluran.

Bisa kididdigar da jaridar Financial Times ta kasar Burtaniya ta yi, kasashen 10 da suka fi yawan al’umma a yankin Latin Amurka, sun riga sun sami alluran rigakafin COVID-19 guda miliyan 143.5, kuma fiye da rabin rigakafin ya isa yankin ne daga kasar Sin.

Kasar Sin ta shiga shirin COVAX na hukumar WHO, ta kuma yi alkawarin samar da alluran rigakafin COVID-19 miliyan 10 a karo na farko, domin biyan bukatun kasashe masu tasowa. Sa’an nan, a ranar 1 ga wata, an fara aikin samar da kashin farko na alluran rigakafin da kasar Sin ta yi alkawarin samarwa shirin COVAX a hukumance.

Haka kuma, an tanadi matakai mafiya sauki na adanawa da raba alluran rigakafin da kamfanin Sinopharm ya samar. Ana iya adana alluran cikin yanayin makin digirin Celcius 2 zuwa makin digirin Celcius 8, ta yadda na’urorin sanyaya kayayyaki da muke da su a halin yanzu, za su iya biyan bukatun adana wannan alluran rigakafi.

Ban da haka kuma, akwai wata ‘yar takardar da ake likawa a jikin kwalabar alluran rigakafin COVID-19 na Sinopharm, wadda take canja launinta bisa yanayin da take ciki, ta yadda ma’aikatan kiwon lafiya za su gane yanayin da alluran rigakafin take ciki.

Kuma, bisa binciken da aka yi wa alluran rigakafin COVID-19 na kamfanin Sinovac, bayan adana alluran cikin yanayin makin digirin Celcius 25 na tsawon kwanaki 42, ko kuma, adana su cikin yanayin makin digirin Celcius 37 cikin tsawon kwanaki 21, ingancin alluran rigakafin ba ya canzawa.

Yanzu, kamfanin Sinovac yana iya samar da alluran rigakafin COVID-19 kimanin biliyan 2 cikin ko wace shekara, kuma, an ba da izni ga kasar Masar, da ta fara sarrafa alluran rigakafi na Sinovac daga watan nan.

Shugaban kamfanin Sinovac Yin Weidong ya bayyana cewa, domin biyan bukatun kasa da kasa, ba kawai muna samar da alluran rigakafi kai tsaye ba ne, har ma muna ba da izni ga wasu kasashe, da su samar da alluran rigakafin, matakan da za su gaggauta aikin samar da rigakafin, yayin da ake rage kudaden da za a kashe kan aikin. Sabo da haka, wasu kasashe za su sami alluran rigakafin COVID-19 cikin sauri, sa’an nan, su yi wa al’ummominsu alluran cikin sauri, ta yadda za a dakile yaduwar annobar cutar COVID-19. Haka kuma, ya ce, kasar Masar tana nahiyar Afirka, inda ake fi fuskantar karancin alluran, don haka ba da iznin samar da rigakafi ga kasar Masar, zai taimaka matuka wajen warware wannan matsala.

A nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kamfanonin kasar wajen samar da fasahohi ga kasashe masu tasowa, da yin hadin gwiwar sarrafa alluran rigakafi, da kuma goyon bayan hukumomin duniya, wajen kawar da ikon mallakar ilmin alluran rigakafin COVID-19, domin inganta aikin samar da alluran rigakafi cikin yanayin adalci tsakanin kasa da kasa. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)