logo

HAUSA

Sin Ta Sha Yabo Game Da Salon Jagorancin Kwamitin Tsaron MDD Na Watan Mayu

2021-06-03 19:47:08 CMG

Sin Ta Sha Yabo Game Da Salon Jagorancin Kwamitin Tsaron MDD Na Watan Mayu_fororder_210603-SHARHI-Saminu

Kamar yadda yake bisa tsari, kasashe mambobin kwamitin tsaron MDD, na jagorantar kwamitin bisa karba-karba, kuma an ga yadda a watan Mayun da ya gabata, kasar Sin ta karbi wannan jagoranci, tare da sauke nauyin dake wuyan ta yadda ya kamata.

Masharhanta da dama na ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, ganin irin yadda Sin din ta taka rawar gani, wajen tabbatar da nasarar shugabancin wannan kwamiti, musamman fannin warware muhimman batutuwa dake jan hankulan sassan kasa da kasa.

A cikin watan na Mayu, kwamitin ya gudanar da ayyuka sama da 30, wadanda suka shafi shawo kan rikicin Isra’ila da Falasdinu, da yunkurin da ake yi na farfadowa, da samar da ci gaban nahiyar Afirka bayan shawo kan annobar COVID-19, da tattaunawa kan matakan kawo karshen tashe tashen hankula a nahiyar, baya ga burin kara jari a ayyukan wanzar da zaman lafiya.

Ko shakka babu, kasar Sin ta yi kokari matuka, wajen yayata muhimmancin cudanyar sassa daban daban, da kare martabar kudurori da dokokin MDD, da ingiza muhawara game da matakan da ake aiwatarwa na yaki da COVID-19, da farfadowar tattalin arzikin duniya bayan annobar, wanda hakan ya sanya kasashe musamman na Afirka, da na Larabawa jinjinawa kasar Sin kwarai da gaske.

A daya bangaren kuma, yayin jagorancin nata, Sin ta gabatar da dabarun kara inganta salon gudanar da ayyukan kwamitin tsaron majalissar, da yin komai ba tare da wata rufa rufa ba, tare da ba da muhimmanci ga sauraron dukkanin sassan masu ruwa da tsaki.

Wadannan dai kadan ne daga tarin ayyuka da Sin ta jagoranta, yayin shugabancin kwamitin tsaron MDDr na watan Mayu, kuma kamar yadda Bahaushe kan ce “yabon gwani ya zama dole”, ayyukan da Sin ta aiwatar a wannan gaba sun shaida manufarta ta tafiya tare da dukkanin sassa, domin cimma moriyar bai daya ga daukacin bil adama. Kuma hakan ya samu yabo daga dukkanin sassan kasa da kasa. (Saminu Hassan)

Saminu