logo

HAUSA

Wayon wasu ‘yan Amurka na shafawa kasar Sin bakin fenti a bayyana yake

2021-06-03 20:16:40 CRI

Wayon wasu ‘yan Amurka na shafawa kasar Sin bakin fenti a bayyana yake_fororder_A

Kwanan nan ne wasu ‘yan Amurka sun sake yada shaci-fadi kan batun da ya shafi asalin kwayar cutar mashako ta COVID-19, inda kafofin watsa labarai da ‘yan siyasa gami da hukumar leken asirin kasar suka hada baki don shafawa kasar Sin bakin fenti.

Amma kowa ya fahimci irin wannan wayon nasu. Tun farko, jaridar The Wall Street Journal ta wallafa wani bayani kafin kaddamar da babban taron WHO, inda a ciki, aka ce wai, an samu wani labari na sirri wanda ke nuna cewa, annobar COVID-19 ta samo asali ne, daga dakin gwajin kwayoyin cututtuka a birnin Wuhan. Sa’annan wasu kafofin watsa labarai sun yi yunkuri yada jita-jitar, har ma wasu ‘yan siyasar Amurka wadanda suka umarci hukumar leken asirin kasar da ta gudanar da bincike. Ta haka ne suka fara yunkurinsu na bata sunan kasar Sin.

Wayon wasu ‘yan Amurka na shafawa kasar Sin bakin fenti a bayyana yake_fororder_B

Har kullum Amurka tana amfani da irin wannan dabara don shafawa kasar Sin bakin fenti, haka ta kitsa karairayi kan batun jihar Xinjiang ta kasar Sin. Wai masana sun bullo da rahoto, sa’annan kafofin watsa labarai suka rura wutar rikici, sai kuma ‘yan siyasar sun yi barazanar gudanar da bincike kan batun.

Karya fura take, ba ta ‘ya’ya. Kowa ya san irin wannan wayo na hukumomin leken asirin Amurka. A nata bangaren, hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta yi gargadin cewa, siyasantar da wannan batu, yana kawo illa ga aikin binciken gano asalin kwayar cutar COVID-19. Kuma manazarta da dama sun yi zargin cewa, abun da ‘yan siyasar Amurka suka yi, wato neman hukumar leken asirin kasar ta jagoranci aikin binciken asalin cutar, ya sabawa tsari na kimiyya kwata-kwata.(Murtala Zhang)