Kamfanin Huawei da jami’ar AAU ta Habasha sun kafa cibiyar horas da fasahar sadarwa
2021-06-02 10:45:56 CRI
Babban kamfanin ayyukan fasahar sadarwa na kasar Sin Huawei, da jam’ar Addis Ababa, wato AAU ta kasar Habasha, sun kaddamar da sabuwar cibiyar samar da horo a fannin fasahohin sadarwa, karkashin tsangayar koyar da ilimin fasaha ta AAiT.
An kafa cibiyar ne da nufin baiwa dalibai da kwararru damar samun horon da ya dace. Kaza lika cibiyar za ta horas da injiniyoyi sama da 2,000, da suka hada da dalibai da malamai a fannin bunkasa kwarewa ayyukan su cikin shekaru 3 masu zuwa.
Da yake jinjinawa muhimmancin wannan cibiya, karamin ministan kimiyya da ilimin gaba da sakandare Mulu Nega, ya ce cibiyar za ta rage gibin da kasar ke da shi na kwarewa, za ta kuma tallafawa kokarin da ake yi na yaye dalibai masu kwazo, wanda hakan zai samarwa Habashan damar bunkasa tattalin arziki mai nasaba da fasahar sadarwa.
A nasa bangaren kuwa, shugaban Jami’ar AAU ta Habasha Tassew Woldehana, cewa ya yi wannan cibiya, da kamfanin Huawei tare da AAU suka kadamar, za ta taka rawar gani wajen baiwa dalibai damar samun irin kwarewar aiki da kasar ke bukata, kamar yadda hakan ke kunshe cikin kudurorin ’yantar da sashen hidimomin sadarwar kasar. (Saminu)