logo

HAUSA

Gudummawar ma’aikatan tabbatar da zaman lafiya a duniya

2021-06-02 08:41:06 CRI

Ranar 29 ga watan Mayun kowace shekara, rana ce ta jami’an wanzar da zaman lafiya ta MDD. Taken ranar ta bana shi ne “hanya mai dorewa ta wanzar da zaman lafiya: sa kaimi ga matasa domin taka rawa wajen shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali”.

Gudummawar ma’aikatan tabbatar da zaman lafiya a duniya_fororder_20210602世界21020-hoto3

Kudirin 57/129 na babban taron MDD ne ya ayyana wannan rana a ranar 11 ga watan Disamba a shekarar 2002. An kuma gudanar da aikin tabbatar da zaman lafiya na MDD na farko a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1948, lokacin da kwamitin sulhun MDD ya amince da tura wata karamar tawagar sojoji zuwa yankin gabas ta tsakiya a matsayin masu sanya ido kan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin Isra’ila da kasashen Larabawa dake makwabtaka da ita.

Kasar Sin ita ce babbar kasa ta biyu dake biyan kudin tallafi da kudin karo karo ga MDD, kuma ita ce kasar da ta fi kowacce ba da adadi mai yawa na dakarun wanzar da zaman lafiya, tun daga shekarar 1990. Wato bayan kasar ta shiga aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, sojoji da ’yan sandanta sun shiga ayyukan kiyaye zaman lafiya har sau 30.

Gudummawar ma’aikatan tabbatar da zaman lafiya a duniya_fororder_20210602世界21020-hoto2

Haka kuma, ta aike da dakarun da yawansu ya kai sama da dubu 50 cikin shekaru 30 da suka gabata. Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasar Sin suna gudanar da ayyukan daidaita rikici da kiyaye kwanciyar hankali da kuma ingiza ci gaban tattalin arziki a kasashe da yankuna sama da 20, ciki har da Cambodiya, da Kongo (Kinshasa), da Liberiya, da Sudan, da Lebanon, da Sudan ta kudu, da Mali, da Afirka ta tsakiya da sauransu.

A halin yanzu, jami’an wanzar da zaman lafiya na kasar Sin sama da 2500 suna ci gaba da gudanar da ayyuka a wurare 8 da kuma hedkwatar MDD.

An karrama jami’an wanzar da zaman lafiya na kasar Sin 413 dake aiki a Mali karkashin MDD, da lambar yabo ta majalisar, bisa irin gudunmawar da suka bayar ga ayyukan tabbatar da zaman lafiya a kasar.

Ana kuma amfani da wannan rana, wajen tuna gudummawar da masu kayan sarki da fararen hula, wadanda suka kwanta dama yayin da suke aikin wanzar da zaman lafiya. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)