logo

HAUSA

Quadri Aruna na Najeriya ya samu gurbin buga gasar Olympics ta birnin Tokyo

2021-06-02 12:02:05 CRI

Quadri Aruna na Najeriya ya samu gurbin buga gasar Olympics ta birnin Tokyo_fororder_210602-Aruna

A jita Talata, hukumar kasa da kasa mai shirya gasar kwallon tebur ko ITTF, ta tabbatar da cewa, kwararren dan wasan kwallon tebur din nan dan Najeriya Quadri Aruna, ya samu gurbin buga gasar Olympic ta birnin Tokyo ta 2020, wadda aka dage gudanarwa zuwa shekarar nan ta 2021.

Da wannan ci gaba, Aruna zai halarci gasar Olympic a karo na 3, bayan da ya wakilci Najeriyar a gasannin shekarun 2012 da kuma 2016.  (Saminu)