logo

HAUSA

Kamata Ya Yi Amurka Ta Kalli Kanta Ta Hada Kai Da Kasa Da Kasa Don Gano Asalin Cutar COVID-19

2021-06-01 20:53:00 CRI

Kamata Ya Yi Amurka Ta Kalli Kanta Ta Hada Kai Da Kasa Da Kasa Don Gano Asalin Cutar COVID-19_fororder_微信图片_20210601203644

An rufe babban taron WHO karo na 74 a yau Talata, yayin taron, wasu ‘yan siyasar Amurka sun nemi shafawa kasar Sin bakin fenti, ta hayar fakewa da batun bincike gano asalin cutar COVID-19.

Tun da Amurka tana nuna shakku kan wannan batu, tana kuma ci gaba da neman shafawa kasar Sin bakin fenti, ya kamata ta amince a gudanar da irin wannan bincike a kasarta ba tare da nuna son kai ba.

Ko shakka babu, dakin gwajin kwayoyin halitta na Fort Detrick shi zai zama wurin farko da za a duba.

Wannan daki an yi masa lakabin “sansanin gwajin sinadarai da tunanin Bil Adama na hukumar leken asiri ta Amurka.” Idan ba a manta ba, an rufe wannan daki a watan Yuli na shekarar 2019, amma ba da dadewa ba, wata cutar dangane da tabar lantarki ta barke a wata unguwa da ba ta da nisa daga wannan daki a jihar Virginia, wadda ta yi kama da cutar COVID-19. Shin me ya sa Amurka ta rufe wannan daki a wancan lokaci? Ko yana da alaka da cutar, ko Amurka ta boye wani abu a cikin wannan daki? Kamata ya yi Amurka ta bude wannan daki don a yi masa cikakken bincike.

A sa’i daya kuma, Amurka ta boye irin wadannan dakunan gwajin halittu fiye da 200 a duniya, ba ta taba bayyana wani abu game da su ba.

Ban da wannan kuma, Amurka ba ta taba bayyana mutum na farko da ya bayyana alamar cutar ba. Alal misali, bisa rahoton da hukumar kiwon lafiya ta gundumar Santa Clara ta jihar California ta bayar, tun daga ran 6 ga watan Fabrairu na shekarar 2020, mutane na mutuwa sakamakon cutar COVID-19, makoni 3 kafin gwamnatin Amurka ta sanar da mamacin farko dangane da cutar. Tsohon shugaban hukumar kandagarkin cututtuka ta Amurka Redfield ya taba bayyana a watan Maris din shekara ta 2020 cewa, mutanen da suka mutu da ake zato a sakamakon mura a watan Satumba na shekarar 2019, hakika cutar COVID-19 ce ta yi ajalinsu . (Amina Xu)